Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuA.A. Zaura: Maganar film Village, yan adawa sun samu wajen fakewa

A.A. Zaura: Maganar film Village, yan adawa sun samu wajen fakewa

A.A ZAURA….MAGANAR FILM VILLAGE. YAN ADAWA SUN SAMI WAJAN FAKEWA

Daga Shariff Aminu Ahlan

Bawani abin mamaki ba ne idan makiya da yan adawa sun yi chaaa akan shahararran dan siyasar nan wanda a yanzu ludayin sa yake kan dawo wajan farin jini da kuma samun karbuwa wajan al’ummar kano da kewaye, in da a kullum dubban jama’a suke tururuwar shigowa tafiyarsa, da yadda yazama abin magana da tauraron sa yake tashe lokaci daya saboda kima, mutunchi, nutsuwa, tausayi da shirin kawo gagarumin chigaba a fadin wannan jiha tamu, asamu wasu yan hassada da ganin kyashi da suke neman abun makusa a gareshi dan su fake da wannan sujawo masa magana. A ganin su hakan ne zai jawo masa chikas da tangarda a tafiyar sa.

- Advertisement -

Tun shigowar sa jam’iyar APC da kuma babbar tarbar da akai masa wanda ba wani dan siyasa a tarihi daya samu irin wannan kyakykyawar karba, sunan A A. Zaura yake mamaye ko ina kamar wutar daji. Hakan tasa wasu da dama daga cikin jam’iyar da kuma yan adawa suka firgita, suka kasa zaune ko tsayuwa, sun kasa gano dalilin wannan dauka da haske da Allah yai masa cikin kankanin lokaci. Da dama kullum hankalin su tashi yake ganin yadda duk inda ka bude kafafan labaran siyasa ko a redio, ko a jaridu ko online media maganar wannan bawan Allah akeyi.

Tun da yashigo jam’iyar APC kullum yabo ne daga dubban al’umma, kuma tsabar kima da mutunchin sa, yan adawa da wadanda suke ganin zai hanasu rawar gabansu, zai zame musu karfan kafa suke ta neman aibinsa ko yaya suzo su yada, amma he is too clean, ya wanku da yawa, an rasa abinda za”a samu a sokeshi. Sun jugum, sun tagumi dan babu makusa bare su fada, kwatsam sai ga dama tazo musu.

Saboda kimarsa, da mutunta kowane irin jama’a da burin bunkasa duk wasu masu neman taimako ta fannin sana”ar su ya rungumi yan film saboda irin gudun mawar da suke badawa. Wanda ba shi kadai bane, duk wani dan siyasa a Nigeria daga shugaban kasa har zuwa chairman suna amfani da yan film dan tallatar ta da manufar su. Wannan abu ne a fili da ba mahalukin da zai musa, saboda Allah ya hore masu dimbin masoya.

Hakan tasa da masu sana’ar suka rungume shi, bai yi kasa a gwiwa ba, yai alkawarin basu gudunmawa wajan bunkasa sana’ar su wanda dubban jama’a ke anfana da ita. Yai alkawarin bada gudun mawarsa wajan bunkasa sana’ar kamar yadda ya shirya tsaf don taimakawa duk wasu masu sana’oi dan cigaban al’umma. To shaukin dadin karramawa da yayi musu wani babba daga chiki mai suna T Y Shaban yafadawa manema labarai cewa A.A. Zaura yai alkawarin gina film village idan yasamu damar dare kujerar Gwamna.

Wannan magana, shauki da dadin karramawa yasa wannan jarumi yafadi wannan magana, amma ba daga A.A. Zaura ba. Saboda an taba niyyar yin hakan lokacin da tsohon dan majilisar tarayya yai niyyar kawo wannan katafaran aiki a Kano.

Lokachi daya akai yiyo cha akansa. Malamai da mutanan gari wadanda basu fahinchi muhimman chin abin ba sukai ta suka da ihun ala tsine. Dole tasa aka fasa aiwatar da abin.
Duk da masana taltalin arziki da shi kansa tsohon Sarkin Kano Sunusi 2 sun kokarin ganar da mutane, amma kasan chewar jama’a sunyi cha akan abin aka watsar da maganar.

To shi T.Y Shaba da duk masu harkar film suna fata da shaukin a samar da Village din saboda cigaban taltalin arziki da samar da aikin yi yasa kullum suke fatan samun film village. Dadin mutun tawa da karramawa da A.A. Zaura yai musu kamar yadda yakewa kowadan ne kungiyoyi suka samu damar ganawa dashi tasa yace A.A. Zaura yace zai gina film village.
Amma wannan magana bata fito daga bakin sa ba, kuma makusan tansa da mai magana da yawunsa a kafafan labarai wato Hon. Mai Huddadu da kuma mai taimaka masa ta harkokin labarai wato Al”amin Chiroma duk sun fito sun nisan tashi da maganar. Sun tabbatar wa duniya bai fada ba, bai kuma wakilta wani ya fadaba, amma ina. Masu neman kuka an jefesu da kashin awaki.
Ba kunya, ba tsoron Allah sai turo masu baki da kunu suke suna surutan wai A A. Zaura yafada. Sai surutai da yamadidi kamar wanda akace zai gina gidan giya.

To daman mun san sun jima suna neman abin kusheshi. To kusake shiri. Bai fadaba, bai kuma sa wani yafada ba. Sai ku koma ku nemo wani abin.

Amma kugane wannan muttum kafin Allah ne, ba kuma wanda zai chanja shirin mai duka ko kankare daukaka da hasken da Allah yai wa bawansa.

A.A. Zaura kafin Allah ne, kuma wannan yarfan ba abinda yajawo masa sai Karin daukaka. Take note. Bai fadaba…Sai kugane CASE CLOSED.

 

 

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: