Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuA.A ZAURA: Masu aikatawa a zahiri ba daya suke da masu suruti...

A.A ZAURA: Masu aikatawa a zahiri ba daya suke da masu suruti ba


DAGA Shariff Aminu Ahlan

Ƴan kaɗan daga cikin ƴan siyasa musamman waɗanda su ke da ƙarfin faɗa aji, da wadatar tattalin arziƙi da masu tasiri su na da kariyar kasancewa masu neman janyo hankalin mutane, amma masu yawan surutu da nuna kansu da yawan maganganu, su kan kai ga bayyana ƙarya da alƙawarorin da ba za su cika ba domin su cimma burinsu na samun wani matsayi ko iko da mulki da shugabancin jama’a. Sai dai, A.A. Zaura Allah ya yi masa albarkar hangen nesa da iya ɗaukan kykkyawar matsayar siyasa da watsi da munanan lamura.

Mutumin ya na buga kykkyawan wasa mai cike da hikima da gamsarwa gami da sakamako mai kyau, wanda ya sha bamban da sauran masu yawan surutu waɗanda kila su na neman mulki ne ido rufe da mummunar manufar neman cimma burukansu kan manufarsu tasu ta su kaɗai don su hau iko da samun dukiya.

Abin ya ban dariya da mamaki matuƙa a lokacin da na karanta wani rubutu a kafar sadarwa ta zamani kwanan nan, inda marubucin ya yi hasashe da nazarin siyasa ya ayyana wasu manyan ƴan siyasa da ake hasashen za su nemi takarar kujera lamba ɗaya ta gwamnan Jihar Kano a 2023. Abin da ya taɓa ni ya kuma ba ni mamaki ya sanya ni dariya shi ne yadda babu inda mrubucin ya sanya sunan mutum mai kykkyawar zuciya da ke da cancantar neman wannan kujera wato shi ne A.A Zaura. Rashin shigar da A.A Zauran tamkar miya ce babu dukkan sinadaran haɗa ta. Amma marubucin ya kamata a yafe masa saboda salon takun mai girma A.A Zaura wanda na faɗa a sama. Hikimarsa da shirunsa da shirinsa na isa ga tudun nasara a nutse, kila shi ne silar da ta sanya marubucin kin sanya shi.

Amma mutum A.A Zaura ba wai ya na neman matsayi ta kowane hali ba ne, amma dai mutum ne mai hankali wanda a kowane lokaci ya ke son samun matsayi bisa cancanta da amincewar mafi rinjayen al’umma masu zaɓe da jam’iyya wanda kuma sannu a hankali ya ke kaiwa gare su ya ke kuma samun karɓuwa da zama abin alfaharin al’umma saboda mutuntakarsa da kyawawan kalamai da ƙwarewa wajen kaiwa ga samun kujerar a 2023. Salon takunsa abu ne mai kyau abin a yaba wanda ya bar da dama da mamaki da kame-kamen sanin abubuwa game da wannan haziƙin matashi mai ƙanƙan da kai da karamci da sauƙin kai mai ƙoƙari da himmar taimakon al’umma a siyasa da wajenta wanda ke da azamar zama na daban a cikin wannan fage.

A lokacin da ƴan siyasa masu madafun iko su ka himmatu wajen maganganu da tura mutane gidajen rediyo dare da rana domin yaɗa musu furofaganda da maganganun ƙarya da rashin hankali, shi kuwa A.A Zaura a kullum sai dai a jiyo al’umma dubbai su na yabo da godiya a gare shi tare da bayya irin yadda ya taimake su ya taba rayuwarsu ta hanyar ba su gudunmawa da kyaututtuka waɗanda su ka taimaka musu wajen sauya musu rayuwa da rage musu raɗaɗin talaucin da su ke fama da shi ta hanyar wakilansa nagari irinsu daraktan yaƙin neman zaɓe, Onarabul Yahaya Garun Ali, Onarabul Ɗahiru Mai-Huddadu da sauran masu taimaka masa ta fannin harkokin sadarwar.

A.A. Zaura ya kasance wanda ya ke samun yabo da godiya daga ɗumbin mabiya da magoya baya wanda hakan ya zamar da shi tauraro a kowane gida, miliyoyin magidanta su ke yi masa addu’ar fatan alkhairi. Wanda hakan ke ƙara bayyana yadda kykkyawan salon siyasarsa ke cigaba da haifar masa da kykkyawan sakamako.

Haƙiƙa ya na cigaba da shafe hasken ƴan siyasa waɗanda a wautar su su ke tunanin za su iya siyen ra’ayin al’umma ta hanyar raba motoci da babura tare da watsi da su. Ta hake ne su ke tunanin mallakar al’umma da siye ƴancinsu da ra’ayinsu da damarsu ta hanyar ba su ɗan wani abu wanda daga ƙarshe za su maida kayansu idan sun kai ga hawa madafun ikonsu. Allah Ya yafe.

A kowane lokaci akwai gamsarwa da ƙayatarwa a duk lokacin da za ka saurari maganganunsa kan shirin siyasa a gidajen Rediyo. Ba su da wani lokaci na kushe da ɓatanci ko yarfe da ƙage ga kowane mai neman takarar siyasa. A mdadin hakan su na maida hankali ne wajen bayyana ayyukan alkhairai na taimakon jama’a da matasa da manufofin siyasa.

Ayyukan taimakon jama’a da ya ke yi waɗanda su ke taɓa rayuwar al’umma kaitsaye sun haɗa da: ba da agaji kan rashin lafiya kyauta ba tare la’akari da bambancin siyasa ba, samar da magunguna da sauran kayayyakin kula da lafiya a dukkannin asibitocin Jiha, ba da tallafin kayayyakin koyo da koyarwa, ɗaukan nauyin karatun yara narasa gata, gina famfunan shan ruwa da gina makarantu na boko da na addini gami da gyara makarantun da su ka lalace. Siyen gidaje da rabar da su kyauta ga mabuƙata da biyawa marasa hali kuɗin gidan haya, ba da tallafin jari ga marasa ƙarfi, tallafawa ƙoƙarin gwamnati a kowane fanni na rayuwa, ba da taimakon abinci da kaya ga gidajen marayu, biyawa ɗaurarru tara domin su samu ƴanci, ba da tallafin abinci da jari ga jama’ara da ke cikin buƙatar taimako da sauran ɗumbin ayyukan alkhairai da dama.

Mutum mai aiki a zahiri ba mai yawan surutu ba. Karin magana ta ce: “Mai yi ba ya faɗa, mai faɗa ba ya yi”. Mu kwatanta cewa waɗannan ɗumbin ayyukan alkhaira ayyuka ne na kashe maƙudan kuɗaɗe da mutumin ya ke kashewa duk da cewar bai taɓa riƙe wani matsayi a gwamnati ba, ya na yi ne da kuɗaɗensa da ya ke kasuwanci ba wai kwasa ya yi daga baitul-mali ba kamar yadda wasu mutanen su ke yi kuma daga ƙarshe kuɗaɗen su koma hannunsu ba.

Idan za mu yi amfani da hankalinmu mu yi nazarin batun, wani mutum guda wanda bai taɓa riƙe wani matsayin gwamnati ba zai himmatu ya maida hankalinsa wajen yin waɗannan ayyukan taimako da jin-ƙai ga al’umma tsawon shekaru ta ƙarƙashin amintacciya, yardaddiyar gidauniyarsa a duniya, A.A Zaura Foundation, idan daga ƙarshe zai zama gwamnan Jiha abin da zai faru ba zai misaltu ba. Ko shakka ba ni yi balle wata fargaba zan iya bugun ƙirji na bayyana cewa zai yi amfani da kuɗaɗen Jiha wajen inganta rayuwar al’umma. Lokacinsa zai zama lokaci na cigaba mai girma tare da kammala ayyukan alkhairan da gwamnati mai ci ta bijiro da su.

Gina al’umma da muhimman ayyukan cigaba, zai ba wa muhimmanci wanda daga ƙarshe zai zama wata kadara da za mu amfana mu kuma yaba gabaɗaya. Tsayayyen mutum wanda ba shakka ya sha bamban da ƴan siyasarmu na wannan zamani waɗanda mafi yawansu su ke neman mulki domin biyan buƙatun kansu gami da watsi da al’ummar da su ka zaɓe su.

Mutum ɗan siyasa mai shiru-shiru da kamun kai, mai sauƙin kai da himmar zama nadaban gami da ƙoƙarin samar da wata moriya da al’umma za su mora har abada. Hirarrakinsa da tattaunawar da ake da shi a kafafen yaɗa labarai maganganunsa da ra’ayoyinsa gami da alƙawuransa ba iri ɗaya ne da na ƴan siyasarmu ba. Amma sauƙaƙan maganganunsa da kykkyawan tunaninsa kan ba da amsa kan fito da komai fili.

Mu mance da batun ɗabi’arsa ta shiru, gogaggen masani ne wanda zai iya riƙe kansa a duk inda ya samu kansa a duniya. Amma har yanzu da sauran lokaci, zai ba da mamaki a duk lokacin da fitaccen ɗan siyasar ya yunƙuro ya fara magana da al’umma kan manufofinsa.

Sai dai a yanzu, babban mutum mai daraja, mai ƙanƙan da kai mai sassauƙan hali, mai karamci, mashahurin gogaggen ɗan kasuwa ɗan siyasa, mai ɗumbin ilimi mai ɗumbin fiƙira na musamman, Zaura ya na yin ayyukansa yadda ake buƙata. Amma ina son duniya ta sani, matashin ɗan siyasar ba wai maida hankali da himmatuwa ya ke da su kaɗai kan manufarsa ba, daɗi da ƙari ya na da duk wani kwaliti na iyawa da cikakken shiri na shiga cikin tarihi.

Sannan kuma a lokacin da burinsa da buƙatarsa da manufarsa na zama na daban su ka tabbata, to a lokacin ne za mu yi farin ciki da godiya ga Allah da ya ba mu wannan bawa nasa mai tawali’u wanda ya ke da kykkyawan ƙudirin ganin Jiharmu ta yi nasara a kowane mataki.

Shariff Aminu Ahlan (Gogaggen Mayaƙin Gwamna Ganduje), rubutawa daga Jihar Kano.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: