Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuA shirye muke mu maida kaki don kawo karshen rashin tsaro a...

A shirye muke mu maida kaki don kawo karshen rashin tsaro a Nigeria –inji Sarkin Zuru

Daga Muryoyi

Sarkin Zuru, Rtd. Manjo Janaral Muhammadu Sani Sami (Sami Gomo II) yace ya fadawa shugaban kasa Muhammadu Buhari a shirye yake ya mayar da kakinsa ya kwashi kayan aiki su shiga fagen daga domin kawo karshen ta’addanci dake addabar kasarnan.

Yace ko a shekarun baya ma kishin kasa yasa suka jajurce domin ganin Nigeria ta zama kasa daya dunkulalliya.

Yace sha’anin tsaro abu ne da ya shafi kowa da kowa ba shugaban kasa kadai ba, “Ni a masarautar Zuru na kafa kwamiti mai karfi kan sha’anin tsaro sannan mun baiwa Gwamnati shawara kuma mun koma bin tsarin da, ko bako yazo gidan mutum sai mai unguwa ya sani”

- Advertisement -

Manjo Janar Sami a tattaunawarsa da Muryoyi a gidansa dake Kaduna, ya ce sha’anin Boko Haram abu ne da za a iya shawo kansa a cikin kankanin lokaci to amma dayake batagarin yan siyasa sun shiga ciki “abun ya zama akwai munafunci shi yasa ya gagara a dakile shi” ya ce a zamaninsu sunyi aiki da zuciya daya, kishin kasar ne a zukatan su shi yasa suka samu nasarar tabbatar da Nigeria kasa daya dunkulalliya “amma yanzu abun ya sha bambam”

Sami wanda aka yaye su a soja a 1963 tare da su Muhammadu Buhari wanda kuma ya rike Gwamna a jihohin Benue, Sokoto da Bauchi a zamanin mulkin soja ya ce Shugaba Muhammadu Buhari yana bakin kokarinsa a kasarnan kuma yafi kowane shugaban kasa kawo cigaba a kasarnan musamman ta fannin samar da ababen more rayuwa.

“Mun ga abubuwa daban daban, kama daga lokacinda akayi juyin mulki a 1966, da lokacinda aka kashe su Murtala, ni na hana su Dimka yin juyin mulki a lokacin bayan sun kashe Murtala nan nasa aka kawo mini gawarsa, sannan nasa aka kaishi dakin ajiye gawa har zuwa lokacinda iyalinsa ta zo”

Muryoyi ta ruwaito da yake magana game da mulkin Zuru, basaraken yace baya cin hanci da rashawa ko danne wa talakawa hakkinsu saboda Allah ya azurtashi da dukiya, “Tun da nayi ritaya a 1990 na fada kasuwanci kuma Allah ya sanya wa kasuwancin Albarka, yanzu haka na samarwa mutane da dama ayyukanyi a Zuru, mun kawo cigaba a fannin ilimi da tsaro, a kalla kowace rana nakan kashe dubban kudade tun hawa na mulki yau kusan shekara 26.” Haka muke ta hidima da jama’a da bukatunsu “kuma mun godewa Allah da ya rufa mana asiri”

A karshe yayi kira ga duka masu rike da madafun iko da su baiwa Shugaba kasa Muhammadu Buhari baya domin inganta kasarnan domin a cewar basaraken bambancin Mulkin soja da na farar hula shine yawan matakai, shi soja ba wasa da ya zartar da doka ta zauna amma a mulkin farar hula sai an bi mataki hakan yasa wasu ke yiwa shuwagabanni zagon kasa ta hanyar sanya siyasa a cikin batutuwan da ya shafi kasa ciki har da tsaro don haka ina kira ga yan majalisar dokoki da Gwamnoni da duka yan siyasa har yan jam’iyyar adawa su marawa Shugaba Muhammadu Buhari baya su bashi dukkan goyon bayan da yake bukata domin ciyar da Nigeria gana.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: