Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuAdam Zango da Ummi Rahab sunyi hannun riga

Adam Zango da Ummi Rahab sunyi hannun riga

Daga Muryoyi

Rahotanni daga masana’antar Kannywood na bayyana cewa dangantaka tayi tsami a tsakanin Jarumi Adam W. Zango da jaruma Ummi Rahab wato wacce ya fara sakawa a fim tun tana yar kankanuwa.

Majiyoyi sun ce abun yayi munin da har jarumin ya cire ta a fim din shi mai dogon zango “Farin wata” inda ya maye gurbin ta da wata bakuwar jarumar.

Muryoyi ta tuntubi Jarumar Ummi Rahab domin jin abunda ya kawo wannan tarnaki amma ta shaida mana cewa “ba zan iya cewa komi ba a yanzu, amma dai nan gaba kadan zan yi karin bayani akai”

- Advertisement -

Muryoyi na dakon martanin Adam Zango da Ummi Rahab dangane da wannan lamari. Dama dai an sha samun jarumi Adamu Zango da samun sabani da mata jarumai kodayake suna shiryawa daga bisani.

Ummi rahab yarinya ce wadda akayi film din kinzamo takwara ummi a shekarun baya.

A lokacin tana karamar yarinya sosai, anan ne ta daina fitowa fina finai inda yanzu sai gata anganta a wani sabon film da Adam a zango ke shirin fitarwa mai suna Farin Wata

Wanda itace zata taka rawa a inda zata zama budurwa shi a akin shirin kamar yadda alamu suka nuna sai dai a yanzu da dangantaka tayi tsami jarumin ya cire ta kwata-kwata daga fim din.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: