Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuAkan wa hakkin matasa ya rataya?

Akan wa hakkin matasa ya rataya?

Daga Fatima S. Abdul

AMFANIN MATASA GA AL’UMMA

Anayi ma matasa kirari da manyan gobe sannan kuma kashin bayan ko wace Al’umma tabbas suna taka rawar gani a al’amuran yau da kullum sannan suna da wani kebantaccen matsayi a kowace Al’umma, kuma sune jagoran ko wace Al’umma

SHIN ME KALMAR MATASA TAKE NUFI?

- Advertisement -

Kalmar matasa tana nufin mutum mai jini a jika ana fara kiran mutum da sunan matashi ne daga shekara 18-35 haka kuma ya danganta da yadda wasu daga cikin mutane suke ganin kuruciyar mutum

AKAN WA HAKKIN MATASA YA RATAYA?

Tabbas hakkin matasa ba akan gwamnati kawai ya rataya ba, harda iyaye da sauran Al’umma baki daya. Saidai gwamnati itace take da babban kaso a ciki, cikin abubuwan da matasa ke bukata daga gwamnati sun hada da, ingattaccen ilimi, lafiya da kuma aikin yi…amma aikin yi shine babban abinda sukafi bukata, domin fitar dasu daga fadawa mummunan rayuwa da kuma kare Al’umma daga samun gurbatattun matasa

Duk Al’ummar da ta rasa matasa na gari to hakika wannan Al’umma ta sami nakasu babba.

Kira ga iyaye, malamai, limamai,sarakuna, pastoci, manya a unguwanni, kunhiyoyi masu zaman Kansu da duk masu fada aji a cikin al’umma …..su kara dagewa wajen nuna ma matasa amfanin su ga Al’umma a addinance, Al’adance da kuma zamanance…

MATASA MANYAN GOBE!

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: