Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuAL’AJABI: Soya kosai haramun ne a Al’adar wani kauye a Abuja

AL’AJABI: Soya kosai haramun ne a Al’adar wani kauye a Abuja

Daga Manuniya

Inda ranka ka sha kallo inji masu iya magana, a yau mun kawo maku rahoton wani kauye ne mai suna Chukuku dake kusa da Gwagwalada a babban birnin tarayya Abuja. Inda al’adar kauyen ta haramta soya kosai kwata-kwata a cikin garin.

Muryoyi ta tattaro daga rahoton NAN cewa mafi yawan mazauna kauyen Gwari ne hade da jefi-jefin kabilar Yarabawa da Inyamurai da kuma Hausawa wanda mafi yawan sana’ar su kuma shine noma.

- Advertisement -

Sarkin kauyen Chukuku, Bikko Usman, ya shaidawa majiyar Muryoyi cewa su ma haka suka taso tun kaka da kakakanni suka tarar da wannan al’ada. Ya ce “amma anyi rangwame mutum na iya fita cen wajen garin ya sayi kosai ya shigo dashi cikin kauyen yaci abunsa amma ba a yarda ya soya kosan a cikin kauyen ba”

Sarkin ya kara da cewa su ma basu san dalili wannan ala’ada ba amma dai haka suka gada kaka da kakanni kuma ba zasu yarda su karya ta ba.

Muryoyi ta ruwaito Sakataren kauyen Chukuku, Sarki Tsugbaza, shima ya bayyana cewa haka aka haifesu suka taso suka tarar tun shekaru aru-aru kuma wasiyya ce daga walidan-walidansu cewa ba’a toya kosai a kauyen.

Wani mazaunin kauyen na Chukuku, Sila Deka, ya ce fiye da shekara 10 yana zaune a kauyen kuma babu wanda ya taba ganin ya soya kosai a kauyen koda kuwa a labari basu taba ji ba domin “haramun ne a bisa ala’adar su”

Sai dai wata mazauniyar kauyen, Junmai Leda, ta ce Kakannin ta sun bata labarin cewa wata mata ce ta taba bacewa bat tana tsakiyar soya kosai a kauyen aka neme ta ko sama ko kasa aka rasa tun daga wannan lokaci kakanninsu suka haramta toya kosai kwata-kwata a kauyen. Kuma har kawo yanzu suna kan wannan wasiyya ta iyaye da kakanni.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: