Amarya ta rasa budurcin ta wajen neman kudin yin “event” din auren ta

Akwai tashin hankali kwarai a wannan labarin.

Na fara rubutawa da turanci, amma na sauya zuwa Hausa saboda sakon ya isa da kyau.

Daga Muryoyi ElhassanTeem Qauran Mata

Dazu na hadu da wani abokina, muna cikin surutai sai yake bani wannan labari me ta yar da hankali.
Yace min a watan Nuwamba 2020, yaje wurin wani mai gidansa,  suna tattauna wata harkar kasuwanci, sun gama suna hira sai aka kira maigidan nasa a waya, sai ya dauka. Mace ce ta kirashi, sai take ce mishi “don Allah Sir, ka kara ko da dubu 20 (₦20,000) ne ya zama dubu 70 (₦70,000) ka taimaka min don Allah, na lissafa yanda ka ce min din, ba naki bane, amma wallahi bazai isheni ba.

- Advertisement -

Sai yace mata, ke, na siya ₦50,000 idan kin siyar, in fada miki lokaci da wuri, abu gashinan baja-baja a gari, saboda ma inaso in taimakeki ne yasa zan bada har ₦50,000 a abunda zan iya samu a dubu daya da dari biyar (₦1500)!

Abokina ya yi zugum bai gane mai ke faruwa ba, bayan sun gama wayan sai Maigidan nasa yake fadamishi.
Wai wannan yar banzan yarinyar, Aure zatayi, mijinta ya bata dubu 50 suje suyi walima, amma ita da kawayen ta da yan uwanta sunce sai anyi shagali “Events” koda Guda biyu ne, yace bashi da hali, bazai bayar ba kuma bazai halarci duk shagalin da suka shirya ba. Da Amaryar suka matsa masa lamba sai anyi ko da event daya ne, yaki amma dai a karshe da ya gaji sai yace ko dai suyi walima ko kuma suje suyi duk abinda zasuyi da wannan dubu 50 din da ya basu, amma shi ba zai kara ko sisi ba.

To saboda Amaryar suna son dole sai anyi event, shine tazo ta roki shi wannan Alhaji yayi Amfani da ita ya bata dubu 100 (₦100,000) ta cika zata sayi wasu designer kaya, da wani special decoration, ta biya MC da DJ, tayi lissafi, tana neman cikon Dubu 100 (₦100,000)!

Shi kuma Alhaji yace abun just few minutes ba zai bayar da dubu 100 ba? Ba ta da hankali, ya koreta, shine ta matsa mishi da waya, har sai da ya gaji yace zai bayar da dubu 50. Shima hamsin din don Budurwa ce jagal babu abinda ya taba gitta ta! Wa’iyazu billah.

Suna cikin haka sai gashi ta kara kira, tace mishi inane zasu hadu? Kuma don Allah yazo dashi Cash, tace masa wai Don Allah idan tazo yau, tazo gobe, zai bata dubu 70 din? Yace A’a, tace mai, ita fa budurwace, bata taba saduwa da wani ba a rayuwarta, idan bacin kaddara da Mijinta ne zai fara saninta nan da yan kwanaki, amma shi zai samu a sama amma bai daraja budurcin ta ya bata dubu 100 ba? Haba ya duba, da kudin da zai rasa, da Abinda zai rasa wanne yafi daraja?

Yace mata kudi yafi daraja, don itama zata siyar da nata abun mai karamin daraja ta karbi kudi, masu babban daraja, idan kuma nata yafi daraja, toh ta tafi ta barmasa nasa, tace to ina zasu hadu?

Ya bata (inda zasu hadu suyi zinar) hotel room da time ya kashe wayarsa.

Abokina yayi jigum ya kasa magana kawai yana sauraren abunda ke wakana tsakanin Alhaji da wannan amarya, nan Alhaji ya bar shi zaune ya tafi hotel abunsa (inda za ta same shi ya yayi zinar da ita).

Innalillahi wainna ilaihirrajiun!
Wannan wane irin masifa ce, akan event ki rasa darajar ki? Kai jama’a, wannan wani irin rayuwa ne? Irin wannan kananan abubuwan da muke kau da kanmu akai muna dauka fa ba abakin komai ba, toh kunji inda suka kai yanzu.

Ya kamata dai a duba, kuma a tashi tsaye da addua, mazanmu da matanmu.

 

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: