Amfanin Kanunfari da ya kamata uwargida ta sani

Amfanin Kanunfari da ya kamata uwargida ta sani

1. Kanunfari yana taimakawa wajan rage sikarin dake cikin jini, to jama’a musamman masu ciwon sikari sai rika yawaita amfani da kanunfari.

2. Ana amfani da kanunfari wajan kawar da tabo a jiki da kuma kuraje

3. Kanunfari na taka muhinmiyar rawa domin yana maganin ko wani irin sanyi a jikin dan-adam musanmam mata ana so mace ta kasan ce ko da yaushe a gidan ta akwai kanunfari ta kuma maida shi kamar shayi domin samu sauki daga cutar sanyi

- Advertisement -

4. Kanunfari na dauke da sinadarin dake rage radadi da kuma kumburi yana da matukar amfanin ga masu ciwon gabobi

5. Yawan san itacen kanunfari zallah na dauke warin baki domin warin baki nada matukar matsala yana hana mutane kusantar mai wannan warin baki, ana so bayan goge baki mutum ya jefa guda daya a bakin shi na akala tsawon minti 20 zuwa 30 domin bada kariya

6. Har ila yau ana amfani da kanunfari domin samar da dandano mai dadi a girki masu girki sunce abinci baya dadi idan ba kanunfari domin sinadaran dake tattara da shi suna taka muhinmiyar rawa.

Wane abu kuke so mu tattauna akai a karo na gana kuna iya tuntuba ta a adreshin mu na email Muryoyinews@gmail.com ko kuma ni marubuciyar wato Aisha Aliyu Shanono aishaaliyu764@gmail.com

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: