Thursday, March 23, 2023
HomeUncategorizedDuba SuAn fasa wani aure da ake tsakiyar daurawa a Kaduna saboda an...

An fasa wani aure da ake tsakiyar daurawa a Kaduna saboda an gano amarya na da HIV

An shiga matsananciyar tashin hankali yau a karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna sakamakon fasa daura wani auren wani matashi Sabiu (mun canza sunansa na asali) da akayi bayan waliyyin amarya da wakilin ango sun hallara har an kammala shigar da siga da komi da komi.

Wakilin Muryoyi wanda ya halarci daura auren da aka yi a wani wuri a garin ya ce bayan an kammala shigar da siga za a daura auren sai mai daurawar ya bukaci a gabatar masa da takardar shaidar gwajin lafiya na Amarya Ramusa’u (mun cenza suna ba sunan ta na asali bane) da Angon ta Sabiu.

Muryoyi ta ruwaito bayan da aka ce babu sai limamin ya ce ba zai daura auren ba sai da takardar lafiya saboda haka ya bukaci za a jira har sai ango da amaryar sunje sunyi gwaji sun kawo masa takardar sahidar asibiti inda nan da nan ango da amarya suka bazama asibiti akayi masu gwaji a mabambantan asibiti.

- Advertisement -

To sai dai bayan wani lokaci sai ango da wakilinsa suka bayyana a wajen daura auren dauke da takardarsu ta shaidar gwaji amma abun mamaki sai aka ji waliyyin amarya shiru.

Muryoyi ta ruwaito nan akayi ta kai ruwa rana har zuwa jimawa amma waliyyin amarya ya ce mahaifiyar amarya taki bashi takardar shaidar lafiyar diyarta har dai daga bisani aka gano ashe sakamakon gwaji ya nuna amarya na dauke da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV.

Wakilin Muryoyi ya ce “Nan da nan aka fasa daura auren inda hayaniya ta kacame amma daga bisani waliyyin amarya suka kira ango da wakilinsa inda suke shaida masa gaskiyar magana sakamakon gwaji ya nuna amarya fa tana dauke da HIV”

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: