An gano mutumin da ya bace shekara 47 daga aikensa shago sayo shinkafa

An gano wani mutum da ya bace tun 1974 daga aikensa shago sayo shinkafa

Daga Muryoyi

Wani mutum a Kenya mai suna James Mwaura dake zaune a garin Molo, a yankin Nakuru ya hadu da iyalansa bayan shafe shekara 47 da bacewa.

- Advertisement -

Muryoyi ta ruwaito an aiki Mwaura tun a 1974 lokacin yana da shekara 23 shago ya sayo shinkafa amma daga nan ba a sake jin duriyarsa ba har anyi cigiya an gaji.

Mista Mwaura, wanda a yanzu yake da shekara 70 yace yayi makuwa ne a lokacin sai dai kwatsam ya tsinci kansa a Nairobi, shikuma daga nan ya wuce garin Naro Moru dake yankin Nyeri ya cigaba da rayuwasa har yayi aure ya haifi yara 3 da jikoki 4.

Mwaura sanye da “bluen taguwa” ya gamu da wani danginsa ne a shafin Facebook wanda suka tattauna har Allah yasa suka gane juna aka kawoshi gida cikin iyalansa.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: