An kai ruwa rana tsakanin musulmi da kirista kan jana’izar wani mamaci a Lagos

Daga Muryoyi

An kai ruwa rana wajen jana’izar fitaccen mai wasan barkwanci na Lagos, Babatunde Omidina, wanda aka fi sani da Baba Suwe, tsakanin musulmi da kirista kan yadda za a bizne mamacin.

Muryoyi ta ruwaito mamacin ya rasu tun a ranar Litinin bayan ya sha fama da jinya. Sai dai wani bangare na iyalai da abokan sana’ar sa da wasu dandazon masoyansa sun hana ayi masa jana’iza kamar yadda addinin musulunci ya gindaya kasancewarsa musulmi.

Cikin abubuwan da ya jawo rudani shine Iyalan sun nemi ba za a yi jana’izarsa a ranar Litinin din da ya rasu ba, sai anyi bukukuwa sannan an jira yanuwa da iyalansa na nesa sun zo sunyi bankwana, sannan a cikin akwaiti suke so a bizne shi, harwayau kuma suka buƙaci zasuyi masa addu’oi a coci kana zasu kewaya da gawarsa kafin a sanya rana ayi masa janaiza.

- Advertisement -

Kodayake dai basu samu nasara ba.

Majiyar Muryoyi ta ruwaito dakyar wani fitaccen malamin addini, Sheikh Ahamad Alfulanny, ya samu aka amshi gawar mamacin akayi mata janaiza a ranar Laraba.

Shehin Malamin ya gaya masu haramcin abubuwan da suke neman yi. Sannan ya fada masu musulinci bai yadda da wannan al’adar ba,

Amma suka ce babu ruwansu da abunda addini ya gindaya saboda a cewarsu ba zai kyautu ace an yi gaggawar bizne fitaccen jarumi kamar Baba Suwe ba, babu wani biki sannan ba a jira iyalansa na nesa sun zo ba, don haka suke bukaci a shirya bukukuwa sannan a sanya shi a akwati.

Malamin yace ya fada masu addini ba ruwansa da ala’ada, dole yadda musulmi ya tsara haka za ayi. Amma dai a karshe musumai sun amshe shi gawar.

Muryoyi ta ruwaito anyi jana’izar margayin da safiyar ranar Laraba kuma an bizne shi ne a kusa da kabarin matarsa, Moladun a cikin gidanshi dake Lagos.

Ayodele Baba Suwe ya rasu yana da shekara 63 a duniya.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: