Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuAn kara farashin mitar wutar lantarki a Nigeria

An kara farashin mitar wutar lantarki a Nigeria

Daga Muryoyi

Hausawa na cewa ana kukan targade sai kuma ga karaya, a lokacinda ake kukan karin farashin mai da na iskar Gass a Nigeria kwatsam kuma sai ga hukumar wutar lantarki ta kara farashin mita.

Daga ranar Litinin 15 ga watan Nuwamba 2021 (wannan makon da muke ciki) yan Nigeria zasu biya karin Naira N13,766 da Naira N26,829 akan kowace mita ta wuta da zasu saya kamar yadda hukumar wuta ta bayyana.

Muryoyi ta ruwaito bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takarda da hukumar wutar lantarkin, NERC ta aikewa duka manajojin wuta a fadin Nigeria.

- Advertisement -

Sanarwar ta ce daga yanzu kudin mita layi daya (one phase) ya tashi daga N44,896.17 zuwa N58,661.69.

Sannan mita mai layi Uku (Three phase) ta tashi daga N82,855.19 zuwa N109,684.36.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: