Daga Muryoyi
Rahotanni da dumi-duminsu na bayyana cewa jami’an tsaro sun samu nasarar kashe Yellow Baba Arusa, kwamandan yan bidiga da ake zargin shi ya jagoranci kai jerin hare-hare a hanyar Kaduna zuwa Abuja ranar Lahadin da ta gabata inda akayi garkuwa da matafiya kana aka kashe wasu.
Majiyar Muryoyi ta ruwaito an kashe kasurgumin dan ta’addan ne a yayin wata musayar wuta da sukayi da yan sanda.
A gefe guda kuma jami’an tsaro sun ce sun kashe wasu manyan yan bindiga 5 a karamar hukumar Kaduna ta Kudu. Muryoyi ta ruwaito jami’an tsaron sun yiwa yan bindigar kwanton bauna ne a lokacinda suka gansu sun je sayo kayan shaye-shaye da kwayoyin kashe zafi na pentazocine.
- Advertisement -