Daga Muryoyi
Kawo yanzu dai shikenan ta kusa tabbata cewa “June 12” ce sabuwar ranar Dimokuradiyya a Nigeria ba “29 May” ba. Domin kuwa majalisun dokokin Nigeria sun amince tare da kokarin kammala yiwa kundin tsarin dokokin Nigeria garambawul domin mayar da 12 ga watan Yuni (June 12) a matsayin sabuwar ranar Dimokuradiyya a Nigeria.
Dama dai a watan Yunin 2018 ne shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana sauya ranar Dimokuradiyya daga 29 ga watan Mayu (29 May) zuwa 12 ga watan Yuni (June 12) domin nuna alhini ga MKO Abiola wanda ake kyautata yakinin shine yaci zaben June 12.
A zaman ta na yau Alhamis Majalisar Dattawa ta yiwa dokar kundin tsarin mulki da ta yi tanadin May 29 a matsayin ranar Dimokuradiyya gyara zuwa June 12. Kuma majalisar tace zata yiwa dokar hutu gyara itama domin a rika yin hutun aiki a duk ranakun June 12 na kowace shekara.