Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuAn sace jaririya daga mai jego ta mika ta raino tayi wanki

An sace jaririya daga mai jego ta mika ta raino tayi wanki

Daga Muryoyi

Al’ummar garin Dakwa, dake yankin Bwari a babban birnin tarayya Abuja sun shiga matsanaciyar damuwa da tashin hankali bayan sace wata jaririya yar watanni Uku da haihuwa mai suna Fatima da akayi a yankin.


Majiyar Muryoyi ta ruwaito cewa mahaifiyar jaririyar mai suna, Talatu Kabiru, take sukola (wankin kaya) sai jaririyar mai suna Fatima ke ta tsala kuka ta hana ta cigaba da sukolar don haka sai ta kira babbar diyarta mai suna Maryam yar shekara 5 ta goya mata jaririyar a baya tace mata ta fita kofar gida suyi wasa domin ta samu ta kammala wankin da take yi.

To sai dai bayan dan lokaci da fitar tasu ne sai ga Maryam ta shigo gida tana kuka inda ta gayawa mahaifiyar tasu cewa suna cikin wasa sai ga wani mutum ya kirawo ta zuwa wani kango ya karbi Fatima sannan yace wa Maryam din ta jira shi zai je ya sayo masu lemu su sha.


Sai sai bayan da Maryam ta mika mashi jaririyar tsawon mintuna bata ga ya dawo ba shine ta rugo gida cikin kuka take shaidawa maman tasu abunda ya faru.


Majiyar Muryoyi ta ce nan da nan mahaifiyar jaririyar ta saki wankin da take yi ta ruga tare da makwafta suka shiga binciken ko ina a unguwar amma babu mutumin babu jaririyar ko kasa. Nan da nan tace sai suka garzaya ofishin yan sanda suka kai rahoto amma kuma aka shaida masu a bisa dokar Nigeria sai bayan awa 48 za a iya daukar wani mataki akai.


Mahaifiyar Jaririyar mai suna Talatu yar kimanin shekara 23 wacce ke cikin tsananin damuwa da firgici ta ce tun ranar 8 ga watan Nuwamba da muke ciki da lamarin ya faru bata dawo hayyacinta ba, domin babu labarin Fatima.

Sai dai ta nemi jama’a su tayasu da addu’oi Allah yasa a gano ta cikin aminci.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: