Za a sanyawa wata Makarantar Yara Marayu da Marasa karfi sunan Yahaya, daya daga cikin matasan nan su 3 ma’aikatan kamfanin Fafutuka da sukayi hadarin mota a Kaduna suka rasu su duka a jajibirin taron kungiyar Arewa Writers Association.
Muryoyi ta ruwaito an samar da makarantar ne domin tunawa da alkhairin da marigayin matashin Yusuf Yahaya Gama yake yiwa marayu a jiharsa ta Kano.
Shugaban Fafutuka Rabiu Biyora ya bayyana haka a shafinsa na Facebook cewa “Za a gudanar da taron saka sunan marigayi Yusuf a wannan makaranta ta Marayu dake Unguwar Rimin Kebe a ranar Asabar mai zuwa, sannan za a gudanar da addu’oi duk a wajen taron..”

- Advertisement -

Muryoyi ta ruwaito za a gudanar da taron ne da misalin karfe 10 na safe in sha Allah, a Rimin Kebe Layin Samaila kusa da massallacin JTI”