Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuAn yankewa wani magidanci hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ya kashe...

An yankewa wani magidanci hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ya kashe dan cikinsa ya sayar

INDA RANKA: An yankewa wani mutum a jihar Adamawa hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ya kashe dan cikinsa ya sayar miliyan 1

Wata kotu a Yola jihar Adamawa ta yankewa wani fulani makiyayi Bappa Alti hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ya kashe dan cikinsa Buba mai shekara 5 da haihuwa ya cire kan sa ya sayar Naira Miliyan Daya.

Muryoyi ta ruwaito a jiya ne alkalin kotun Justice Fatima Ahmed Tafida ta yankewa Bappa Alti, hukuncin bayan an kammala bincike kan gora, da adda da kuma gano gawa da gangan jikin mamacin sannan shi da kansa ya fadi ya aikata laifin.

- Advertisement -

Lamarin dai ya faru ne a kauyen Ganji dake karamar hukumar Gombi, inda mahaifin yaron ya tafi dashi gona kiwo sannan ya sa gora ya make shi, bayan yaron ya suma sai ya saka adda ya sare kansa sannan ya kai a bashi Naira miliyan Daya.

Bappa ya ce tun da farko wani ne mai suna Alhaji Sange ya ce masa ya kawo masa kan mutum zai bashi Naira miliyan Daya shi yasa ya yanke shawarar sare na dan cikinsa ya kai.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: