Anyi auren budurwar da aka ce wai tana da HIV har aka fasa aurenta ana tsakiyar daurawa

A karshe dai gaskiya tayi halinta domin kuwa an daura auren Rashida Nuhu Abubakar da Angonta Sagir amaryar da aka yiwa sharrin tana da HIV, aka fasa daura aurenta ana tsakiyar daurawa.

A ranar Asabar 19 ga watan Disamba 2020 an hallara an fara haramar daura auren Rashida da angonta Sagir har an shigar da siga sai kwatsam madaurin auren ya ce a bashi takardar shaidar lafiyar ango da na amarya

Amarya sha kushe Malama Rashida a cikin alkyabba bayan daura aure

Bayan ya fahimci babu sai ya nemi su je suyi gwaji yanzu su dawo sai a kawo masa satifiket din gwajin sannan zai daura auren,

- Advertisement -

Muryoyi ta ruwaito jim kadan sai ga wakilin ango ya zo da nashi satifiket amma akaji waliyyin amarya shiru lamarin da ya jawo rudani har dai aka bayyanawa wakilin ango cewa yayi hakuri domin kuwa sakamakon gwaji ya nuna amarya na dauke da HIV, nan da nan aka fasa auren kowa ya watse cike da ta’ajibi. Kowa na fadin albarkacin bakinsa.

To sai dai Muryoyi ta bi diddigin labarin inda ta samu anyi bincike an gano makirci ne aka shiryawa amaryar lamarin da ya jawo aka je aka sake gwaji wanda sakamako ya nuna lafiyar Rashida kalau.

Binciken farko dai ya nuna an yi hadin baki ne ysakanin wani tsohon saurayinta wanda cikin danginta yake sannan da hadin bakin wasu dangin nata da basu so ayi auren ne suka musanya takardar gwajin nata.

Amarya Rashida a yayin liyafar bikin nata

Manuniya ta ruwaito bayan wannan sabon bayani ne sai dangin ango da amaryar suka hadu ba bata lokaci aka daura auren masoyan wadanda a lokacin ke cike da tashin hankali aka daura da misalin karfe 10 na safiyar ranar Talata 22/12/2020 a NDC Kaduna.

Rashida da angonta Sagir

Daya daga cikin yayyin amaryar mai suna Abubakar Nuhu Abubakar ya shaidawa Manuniya cewa “Wannan abu ya matukar bamu mamaki amma Alhamdulillah tunda a karshe gaskiya tayi halinta, wadanda suka shirya wannan manakisa kuma mun barsu da Allah sannan mun mika maganar ana kan bincike domin daukar matakin da ya dace akansu”

Taron daura auren ya samu tagomashi sosai domin kuwa dandazon jama’a ne yanuwa da masu taya amarya da ango alhini suka yi cincirindo aka daura shi.

“Alhamdulillah mun godewa Allah kuma yanzu haka amarya ta shiga dakin mijinta, muna godiya da addu’oi da fatan alkhairi da yan’uwa da sauran jama’a suka yi taya mu,” inji daya Yayan Amarya, Turaki.

Cike da farin ciki da annushawa an sha biki, bayan kammala daura aure kowa na nuna farin cikinsa saboda murna baki har kunne.

Manuniya ta ruwaito an ci an sha an gyagije a wajen walima da liyafar auren kana daga bisani aka kai amarya Malama Rashida dakin angonta Malam Sagir cike da annushawa.

Muna roko Allah ya rabamu da sharrin yan uba, yan’uwa da duka sharrin wanda muka sani da bamu sani ba

 

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: