Daga Muryoyi
Gwamnatin Nigeria ta ce tayi farinciki sosai da babbar kotun Abuja ta ayyana yan fashin daji da yan bindiga da masu garkuwa da mutane a matsayin yan ta’adda.
Muryoyi ta ruwaito a wata sanarwa da ministan Shara’a na kasa Abubakar Malami SAN ya fitar ranar Juma’a ya ce a yanzu Gwamnatin tarayya zata saki jiki ta ragargaji yan ta’addan ba kakkautawa.
A cewar minstan ofishinsa ne ya shigar da bukatar a gaban kotu. Kuma yayi hakan ne domin nunawa duniya yadda Gwamnatin Nigeria ke taka-tsantsan da kuma bin dokokin yaki da tabbatar da ba a take hakki ko cin zarafin kowa ba.
- Advertisement -
Amma hukuncin na kotu a yanzu inji Malami ya basu dama zasu hadu da duka hukumomi da suka dace domin ganin an haramta kungiyar kana an fatattake su ta halin ko ‘kaka.