Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuAyyana yan fashin daji a matsayin yan ta'adda ba zai cenza komi...

Ayyana yan fashin daji a matsayin yan ta’adda ba zai cenza komi ba –inji Sheikh Gumi

Daga Muryoyi

Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Ahamad Gumi ya yi fatali da matakin da Gwamnatin Nigeria ta dauka na ayyana yan fashin daji da masu garkuwa da mutane a matsayin yan ta’addan domin a cewarsa wannan mataki ba zai cenza komi ba game da matsalar tsaron da ake fuskanta a kasar.

Wata babbar Kotu a Abuja ce dai a karkashin mai shara’a Justice Taiwo Taiwo ta ayyana yan fashin daji da Yan Bindiga a matsayin yan ta’adda wanda hakan ke nufin Gwamnatin Nigeria za ta iya amfani da duka muggan makamai wajen yakarsu da karkashe su ba tare da katsalandan din kasashen duniya ba.

To sai dai Sheikh Gumi a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a ta bakin mai magana da yawunsa, Malam Tukur Mamu (Dan-Iyan Fika) ya ce wannan mataki ba zai yi tasiri ba domin ko a baya Gwamnatin tarayya ta ayyana yan IPOP masu rajin kafa kasar biyafara a matsayin yan ta’adda amma hakan bai sauya komi ba hasali ma ko kasashen duniya babu wacce ta amshi wannan umurni na Gwamnatin Nigeria.

- Advertisement -

Muryoyi ta ruwaito Shehin Malamin ya ce “Yan IPOP din sun cigaba da harkokin su da walwalarsu Kazalika sun cigaba da kaddamar da hare-hare kan jami’an tsaro da kashe yan Arewa da sauran ayyukan ta’addanci.

Ba kowane Fulani bane dan ta’adda,

Gumi ya ce ina yana fata yan Nigeria ba zasu yi amfani da wannan dama ba wajen kashe al’ummar Fulani makiyaya da basu ji ba basu gani ba, Aikin wasu yan tsiraru cikinsu bai kamata ya zama lasisin kyamatarsu ko kashe su baki daya ba ayi masu yadda akayi wa yan IPOB domin Fulani ma al’umma ce mai yanci kuma su ma cikakkun yan kasa ne.

“Idan kuwa aka rika daukar doka a hannu kan Fulanin to lallai ba zai haifarwa da kasarnan da mai ido ba” inji Gumi

“Mun fadawa Gwamnati rikicin yan fashin daji abu ne wanda za a iya magancewa cikin ruwan sanyi, ta hanyar yi masu adalci sannan da zama a teburin Sulhu dasu kamar yadda akayiwa yan taratsin Neja Delta,”

“Idan zamu yi wa kanmu adalci kafin rikicin yan fashin daji da a yanzu ya addabe mu, ai a baya Fulani makiyaya sun ji jiki musamman a hannun hukumomi.

Aka rika yi masu kwacen shanu aka hana su kiwo da dai sauran kuntatawa. Don haka ya kamata a zauna teburin sulhu dasu a saurari bukatunsu, a kula da iliminsu a janyo su a jiki kamar yadda akewa kowace kabila a kasarnan domin su ma yan kasa ne,” inji Dr Ahmed Gumi

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: