Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuBabu sauran yin uzuri ga Shugaban kasa a wannan lokacin

Babu sauran yin uzuri ga Shugaban kasa a wannan lokacin

Daga Yasir Ramadan Gwale
(29-11-2020)

Duk wadannan abubuwan da suke faruwa na tashin hankali da kashe kashe a yankin Arewacin Najeriya, Shugaban kasa ya bada kofar faruwarsu. A farkon al’amari an yi zaton cewar shi din wani jajirtacce ne da ba zai zauna a fadar Gwamnati a Abuja cikin sanyi da kayan ciye ciye iri iri ba, yayi Likimo yana kallon Najeriya a Computer ana karanta masa rahotanni na gaskiya da wadan da ba na gaskiya ba.

Mun yi zaton Shugaba Buhari zai zama Kamar Gwamna Zulum ne wajen bibiya dan sanin halin da kasa da kuma al’umma suke ciki, Amma sai muka ga akasi. Gwamna Zulum da bamu yi tsammanin zai yi rabin kokarin da yake yi ba, sai gash kullum yana nuna misalin Shugabanci na adalci da kokarin kamantawa. Amma shugaba Buhari da muka sa masa ran zai yi abinda Gwama Zulum yake sai gashi ya bamu kunya.

Babu sauran yin uzuri ga Shugaban kasa a wannan lokacin. Najeriya na cikin matsananciyar Matsalar tsaro wadda dukkan alamu suke nuna cewar matsalar tafi Karfin Gwamnatin Najeriya ita kadai. Dan Haka, abinda ya dace kuma ya kamata ayi, shi ne, shugaban kasa yayi yekuwar Neman taimakon kasashen Duniya musamman makobta domin fuskantar wannan barazana ta Boko Haram da kuma gurbatattun mutane da suke daukar nauyin kashe kashen da ake yi a kauyuka da garuruwa.

- Advertisement -

Ba zai yuwu Shugaban kasa ya cigaba da zama a fadar Gwamnati cikin daula a Abuja yana jaje da yin Allahwadai bai ba, dole ya tashi ya je inda ake wadannan kashe kashe ya ganewa idonsa ko a dauki matakin da ya dace, Amma zama a fadar Shugaban kasa kurum ana gaya masa labari Yana cewa ya kadu ko ya damu, ba zai yuwu ba.

Lallai ya zama wajibi Shugaban kasa yaje #Zabarmari domin jajantawa Gwamnatin jihar Borno da Al’ummar da aka kashewa dangi da ‘yan uwansu a wannan mummunan harin ta’addanci. Ya kamata wadannan kashe kashe su zo karshe. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ka san fa Annabi ya faku. Babu wani wahayi da zai zo yace kai ba kada laifi ko kai Mai gaskiya ne. Dole ka tashi ka kawo karshen zubar da jini, idan ba Haka ba, ka nemi afuwar ‘yan Najeriya ka sauka. Domin wallahi Shugabanci Amana ce kuma ko gaban Allah ba zaka tsira ba a irin wannan hali da ake ciki na zubar da jinin bayin Allah da Basu ji ba, basu gani ba. Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: