Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuBiloniyan China Jack mai Alibaba ya bata tun bayan da ya soki...

Biloniyan China Jack mai Alibaba ya bata tun bayan da ya soki Gwamnatin kasar

Duniyar kimiyya da fasaha ta shiga dar-dar sakamakon batan ko sama ko kasa da shugaban kamfanin kimiyya da fasaha da kere-kere na kasar China Alibaba Group Holding kana hamshakin mai kudi na kasar China Jack Ma yayi tun watan Octoba.

Muryoyi ta ruwaito a ranar 24 ga watan Octoba 2020 Bilioniya Jack a yayin wani jawabi da yayi ya soki Gwamnatin kasar China a karkashin Shugaba Xi Jinping game da yadda take tafiyar da tattalin arzikin kasar.

Sai dai tun daga wannan lokacin Shugaba Xi ya saka kafan wando daya dashi har ta kai ga an kafa kwamiti an fara binciken kamfanin sa na Alibaba Group Holding.

- Advertisement -

Kana kuma Gwamnatin kasar China ta umurci Mista Jack Ma kada ya sake ya fita daga kasar har sai an kammala wasu bincike akansa.

A watan Nuwamba 2020 aka kwashe dala Biliyan $10 daga asusun kamfaninsa kana kuma aka gindaya masa wasu sharudda.

Yau fiye da wata Biyu ba a sake jin duriyar Mista Jack Ma ba kana kuma duk wasu tarurruka da ya kamata ya je sai dai wasu ke wakiltarsa, hatta ma wani taron shekara da yake yi a wannan karon wani ne ya jagoranci taron. Wannan ya sa hankula sun tashi an fara zargin Mac ya bata

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: