IBB ya bayyana wanda zai gaji Buhari a 2023

Daga Muryoyi

Tsohon shugaban Nigeria Janaral Ibrahim Babangida, yace ya ga wani matashi da shekarunsa basu shige 60 ba amma ya hada duk wata Nagarta da cancanta ta shugabanci irin wanda Nigeria ke so,

Muryoyi ta ruwaito IBB a tattaunawarsa da Arise TV, ya shawarci yan Nigeria kada su sake su zabi wanda ya haura shekara 60 a matsayin shugaban kasa a 2023.

Ya ce Nigeria tana bukatar shugaba wanda yake da jini a jika, sannan wanda yake da kwarewa a fannin tattalin arziki da salon mulki da shugabanci na zamani wanda ya iya siyasa kuma yake da abokai a duka sassan kasarnan,

- Advertisement -

Muryoyi ta ruwaito tsohon shugaban na cewa rashin shuwagabanni nagari shine babban dalilin da ya jawo ma Nigeria koma baya ta fuskar tattalin arziki da saukin rayuwa.

“Ina yiwa Nigeria sha’awar shugaba mai ilimi, dan siyasa wanda ya iya tafiyar da al’umma sannan yake da abokai a kowane sashi na kasar nan, naga akalla mutum 1 zuwa 2 zuwa 3 wanda ya hada duk wadannan cancantar, wani ne bai shige shekara 60 ba, kuma na tabbatar zai lashe zabe indai aka bashi dama yayi takara.” inji IBB

Kawo yanzu dai manyan wadanda ake ganin sun kwallafa rai kan shugabancin Nigeria a 2023 sune jagoran APC, Ahmed Bola Tinubu da Atiku Abubakar wanda kuma dukkansu sun haura shekara 60, wa kuke ganin IBB yake nufi?

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: