Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuBuhari naso kamfanin Twitter ya biya asarar da Nigeria tayi a zanga-zangar...

Buhari naso kamfanin Twitter ya biya asarar da Nigeria tayi a zanga-zangar EndSars

Gwamnatin Nigeria naso kamfanin Twitter ya biya asarar da kasar ta tafka a zanga-zangar EndSars

Daga Muryoyi

Gwamnatin Nigeria ta ce da yuwuwar ta gurfanar da kamfanin Twitter da shugabanta Jack Dorsey a gaban kuliya domin ya biya dumbin asarar da Nigeria tayi a yayin zanga-zangarENDSARS.

- Advertisement -

Ministan yada labarai ya ce shugaban Twitter ya tara wa masu zanga-zangar EndSars kudade sannan ya kirkiro wani tambari na musamman a Twitter domin karfafa masu zanga-zangar EndSars. Uwa uba kuma ya bawa masu zanga-zangar dukkan wata gudummuwa domin ganin abunda ya faru ya faru.

Muryoyi ta ruwaito Ministan na lissafo cewa kadan daga cikin asarar da zanga-zangar EndSars ta jawo ya hada da asarar rayuka ciki har da mutuwar yan sanda 37, Sojoji 6 sun mutu, fararen hula 57 sun mutu sannan an lalata dukiya ta Biliyoyin Naira.

Bugu da kari an lalata motocin yan sanda akalla guda 164 an kona ofisoshin yan sanda guda 134 an farfasa kamfanoni masu zaman kansu akalla guda, 265 sannan an farfasa kamfanonin Gwamnati akalla guda 243

Alhaji Lai ya kuma ce an fasa rumbunan ajiyar abinci akalla guda 81 sannan an kone kurmus sabbin manyan motocin safa fiye da 200 da Gwamnatin Lagos ta sayo.

Ana dai ganin Gwamnatin Nigeria zata tilasta kamfanin na Twitter sai ya biya wadannan asarori da kasar ta tafka kafin janye takunkumin da aka sanya masa a Nigeria.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: