Buhari yace an kusa daina zaman makoki da juyayi a saboda rashin tsaro a Nigeria

Daga Muryoyi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa yan Nigeria tabbacin cewa nan gaba kadan za a daina kukan juyayi da zaman makoki na rashin rayuka da dukiya a sanadiyyar rashin tsaro a kasar,

Shugaban kasar ya bayyana haka ne cikin wata ta’aziyya da ya fitar zuwa ga iyalan wasu yan sanda da yan IPOP suka dauki bidiyo suna kashewa da kuma daukacin wadanda suka rasa wasu nasu a sakamakon harin ta’addanci a kasar.

Ya ce abun bakin ciki ne da takaici yadda zukatan wasu suka dusashe suka bushe suka cika da bakin ciki da kiyayya ga yan uwansu yan Adam.

- Advertisement -

Muryoyi ta ruwaito Buhari yayi addu’a Allah ya jikan yan sandan da sauran wadanda harin ta’addanci ya rutsa sannan ya bada tabbacin cewa kamar yadda zaman lafiya da walwala ya komo a wasu wurare da a baya sukayi fama da hare-haren ta’addanci to haka zaman lafiya da walwala zai dawo ko ina a sassan kasarnan.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: