Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuBurina mu kammala wa'adin mulkin mu ana kewar mu --El-Rufai

Burina mu kammala wa’adin mulkin mu ana kewar mu –El-Rufai

Daga Mur

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa yana gudanar da sauye-sauyen wajen aiki ne ga mukarrabansa domin su samu ilimi da kwarewa kan kowane fanni na sha’anin gudanar da mulki ba kawai su zauna a ma’aikata ko guri daya ba shekara da shekaru.

Gwayana ya ce yana fata anan gaba a samu Gwamna a cikin mukarraban nasa domin yasan kwarewar da suka samu ya basu kwarin guiwa da cancantar gudanar da aiki yadda ya kamata.

Muryoyi ta ruwaito Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da yake gudanar da bikin rantsar da sabbin Alkalai da Kwamishinonin da ya nada.

- Advertisement -

A makon da ya gabata ne dai Gwamnan ya yi garanbawul ga majalisar jihar Kaduna, inda ya mayar da wasu Kwamishinoni zuwa wasu guraben sannan ya sauyawa wasu shugabanin hukumomin Gwamnatin guraben ayyuka tare da nada wasu.

Hakan ya janyo cece-kuce wanda ake ganin tamkar ya ragewa wasu daga cikinsu matsayi ne, alal misali shugaban ma’aikata fadar Gwamnati, Muhammad Abdullahi Dattijo an mayar da shi Kwamishinan Kasafin kudi da tsare-tsare, kana an mayar da shugabar zuba jari, KADIPA, Umma Aboki zuwa Sakatariyar din-din a ma’aikatar kasafi da tsare-tsare.

Sai kuma uwa uba Gwamnan ya nada wasu sabbin Kwamishinoni uku da ya ce zasu kula da sabbin hukumar kula da birane da ya kirkiro a jihar,  Kaduna ta tsakiya, Kafanchan da Zaria.

Sai dai El-Rufai ya yi karin haske cewa dama akwai wadannan hukumomin a tsarin jihar kafin aka rusa dokar, kuma yanzu sun ga cewa maido da wannan tsari shine mafita domin bunkasa wadannan birane.

A cewar Gwamnan, yana matukar wahala a iya cimma abunda ake so a karkashin ma’aikatar kula da kananan hukumomi wanda hakan tasa a lokacin da yake ministan babban birnin tarayya, El-Rufai ya bawa shugaban kasa na lokacin, Olusegun Obasanjo shawara ya kirkiri hukumar kula da birnin tarayya, FCTA.

Gwamnan ya ce Kwatankwacin hakan ne yayi anan Kaduna, kuma matsayin sabbin Kwamishinonin biranen daidai yake da na ministan Abuja. “Muna fata wadanda muka nada din zasu fitar da mu kunya ta hanyar yin aiki tukuru, za mu basu dukkan goyon bayan da suke bukata”

‘Daga mai wanke bandaki da goge-goge har zuwa Kwamishinoni da ni kaina Gwamnan matsayin mu daya a sha’anin Gwamnati don haka ko ina aka tura mutum duk cikin aiki ne. Fatan mu shine Allah ya bamu iko mu sauke nauyin da muka dauka, mu samu mu karasa watanni 19 da suka rage mana cikin aminci kamar yadda muka fara mulkin mu a 2015 cikin aminci. Fatan mu shine mu cika burin jama’ar Kaduna kamar yadda suka zabe mu’ inji shi

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: