Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuCututtuka guda 9 masu matukar illa da shaye-shaye ke haifar dasu

Cututtuka guda 9 masu matukar illa da shaye-shaye ke haifar dasu

Daga Fatima S. Abdul

Shaye shaye ya zama ruwan dare a wannan zamanin musamman a tsakanin matasa wanda babu maza babu mata.

Da yawan matasa dake shaye shaye suna fadawa wannan bala’i ne ta hanyar hulda da abokan banza….

 

- Advertisement -

ABUBUWAN DAKE JEFA MATASA GA SHAYE SHAYE

Abubuwan dake jefa matasan a harkar shaye shaye suna da yawa amma ga kadan daga ciki zan kawo maku:

1: Jahilci
2: Talauci
3: Sakacin iyaye
4: Rashin aikin yi
5: Aikin karfi
6: Hulda da abokanan banza
7: Son zuciya
8: Samun kayan mayen a cikin sauki da dai sauran su

ILLOLIN DA SHAYE SHAYE KE HADDASAWA

1: Ciwon hauka
2: Ciwon huhu
3: Ciwon sanyi
4: Ciwon kansa
5: Ciwon hanta
6: Kazanta
7: Yawan tunani mai tsanani da muni wanda ka iya sanya hawan jini ko ciwon zuciya
8: Sanya lalaci ta yadda mutum ba zai iya aikata komi ba har sai yayi shaye shayen
9: Jefa mutum cikin miyagun ayyuka kamar sata, fashi da sauransu

HANYOYIN DA ZA A BI WURIN MAGANCE SHAYE SHAYE TSAKANIN MATASA

Duk da cewa gwamnati na iya bakin kokarinta wurin sanya matakan tsaro domin kawo karshen wannan annoba, yakamata iyaye su sanya ido akan yaransu su san halin da suke ciki da kuma irin aboka nan da suke hulda dasu. Sannan kuma Malamai da limamai da pastoci da kuma manya da dattawa a unguwanni su dage wurin nuna illolin shaye shaye a al’adance da kuma addinance.

Taba ta tabbata a barta duk da masu shanta basu barta ba. masana kiwon lafiya sun bada tabbacin cewa mashaya suna mutuwa da kuruciyar su.

Allah ya yaye mana wannan fitina ta shaye-shaye, sai mun hadu a maudu’i na gaba daga yar’uwar ku Fatima S. Abdul. Me kuke so mu tattauna akai, kuyi mana (Tes kawai) a 07062651273

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: