Thursday, March 23, 2023
HomeUncategorizedDuba SuDA DUMI-DUMI: El-Rufai ya rage aikin Gwamnati a Kaduna zuwa kwana 4...

DA DUMI-DUMI: El-Rufai ya rage aikin Gwamnati a Kaduna zuwa kwana 4 a mako

Daga Muryoyi

Gwamnatin jihar Kaduna ta rage ranakun ayyukan Gwamnati a jihar zuwa kwana 4 a wani mataki na garambawul da sanya aikin Gwamnatin zuwa wani mataki,

A wata sanarwa da kakakin Gwamnam jihar Kaduna, Muyiwa Adekeye ya fitar ya ce daga yanzu ranakun aiki a duka fadin jihar ya koma karfe 8 na safe zuwa 5 na yamma Litinin zuwa Juma’a,

Muryoyi ta ruwaito amma kuma in banda ma’aikatan fannin ilimi da lafiya kowance ma’aikaci zai zauna a gida a ranakun Juma’a domin ya kula da iyalansa da wasu ayyukan noma da ga masu sha’awa.

- Advertisement -

Muyiwa ya ce shirye-shirye sunyi nisa domin ganin su ma fannin ma’aikatu masu zaman kansu sun bi wannan sabon salo na aiki, hakanan su ma ma’aikatan kiwon lafiya da ilimi zasu shiga wannan tsari nan gaba kadan, Elrufai yace suna kokarin zamanantar da yanayin aiki a jihar Kaduna ta yadda za a rika amfani da fasahar zamani wajen gudanar da manyan ayyuka

Sabon kudurin zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Disamba 2021.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: