Daga Muryoyi
Gwamnatin jihar Kaduna ta janye matakin da ta dauka na rufe hanyoyin sadarwa a wasu sassan jihar. Daga yau Juma’a za a bude duka hanyoyin sadarwa a ko ina a fadin jihar Kaduna.
Muryoyi ta ruwaito sai dai Gwamnatin ta ce sauran matakan da ta dauka suna nan drama, kamar hana zirga-zirga da babura masu kafa biyu, da sayar da mai a jarka a wasu kananan hukumomi dake jihar da cin kasuwannin mako mako da kuma sayar da dabbobi. Wadannan dokokin zasu cigaba da aiki har sai yadda hali yayi.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka a wata sanarwa da fitar yau Juma’a.
- Advertisement -
Gwamna El-Rufai ya baiwa jama’ar jihar hakuri bisa wannan mataki wanda yace daukarsa ya zama wajibi saboda tsaron dukiya da rayukan jama’a, sai dai Aruwan ya bayyana cewa an samu gagarumar nasara a dan lokacin da aka katse layukan sadarwar.