Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuDA DUMI-DUMI: Kotu ta ci tarar Gwamnatin Kano ta biya Sanusi Miliyan...

DA DUMI-DUMI: Kotu ta ci tarar Gwamnatin Kano ta biya Sanusi Miliyan N10 bisa fitar dashi daga Kano

Daga Muryoyi

Wata babbar kotu a Abuja ta yanke hukunci a biya Sarkin Kano na 14, Muhammad Sanusi II tarar Naira Miliyan 10 saboda aika shi da akayi daga jihar Kano zuwa wata jihar aka killace shi bayan Gwamnati ta sauke shi daga Sarautar Sarkin Kano,

Justice Anwuli Chikere, ne ta yanke hukuncin a yau Talata inda tace dokar masarautar Kano 2019 da akayi amfani da ita wajen killace Sarkin ta ci karo da kundin tsarin mulki na Nigeria 1999.

A cewar Alkali Chikere, kundin tsarin mulkin Nigeria shine gaba da komi don haka hana Sarki Sanusi zuwa Kano ko daukarsa zuwa wani waje haramun ne a dokar Nigeria. Sarkin yana da damar zuwa Kano da duk inda yaso watayawa.

- Advertisement -

Muryoyi ta ruwaito Muhammadu Sanusi ne dai ya shigar da kara gaban Kotu domin kalubalanatar rundunar yan sanda da ta DSS da Gwamnatin Kano killace shi.

Kotun ta ce baya ga tarar Naira Miliyan 10 dole Gwamnatin ta baiwa Sarkin hakuri a rubuce a cikin akalla jaridun kasar guda Biyu.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: