Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuDalibin ajin karshe a jami'ar Ilorin ya yiwa wata lakcara jina-jina

Dalibin ajin karshe a jami’ar Ilorin ya yiwa wata lakcara jina-jina

Daga Muryoyi

Wani dalibin ajin karshe (400 Level) a jam’iar Ilorin dake jihar Kwara, (Unilorin) dake karantar Microbiology, Abdulwaheed Waliu, (Captain Waliu) ya yiwa wata Lakcara mai suna Misis Sakariyah jina-jina saboda taki daga masa kafa kan wani atisaye da bai yi ba.

Jaridar Muryoyi ta bi diddigin rahoton kuma ta ruwaito dalibin ya iske Malamar Misis Sakariyah har Ofishinta ya nemi ta taimaka masa kan wani aikin dalibai na wajibi “Industrial Work Scheme (SIWES) da bai samu yayi ba kuma dama ita ce aka wakilta ta duba aikin nasa wato “Project Supervisor dinsa”

Sai dai ga dukkan alamu Malamar taki bashi hadin kai abunda ya fusata shi tun yana mata ihu yana bubbuga tebur har ta kai ga ya fara sharara mata mari. Bayan yaga ta kidime ta fara kururuwa sai dalibin ya dora da gabza mata naushi, Muryoyi ta ruwaito dakyar lakcarar ta kubuce ta fita a guje zuwa tsakiyar jami’ar tana ihu tana neman taimako amma dalibin ya bita ya cigaba da dukan ta har ta zame ta fadi kasa yana naushin ta, nan da nan tayi jina-jina.

- Advertisement -

Yadda aka kwashi malamar jina-jina a harabar jami’ar bayan an kawo mata dauki

A bidiyon da Muryoyi ta kalla ta ga Malamar warwas a kasa dalibin yana ta dukan ta kafin Dalibai da Malaman Jami’ar suka ankara da abunda ke faruwa suka ruga a guje domin kai mata dauki. Nan da nan sai dalibin ya ruga a guje aka bi shi har aka samu nasarar kama shi. Ita kuma aka kaita wani asibiti dake Jami’ar domin kulawa da lafiyar ta.

Kodayake dai Malamar na samun sauki amma shugaban sashin dalibai na jami’ar Kunle Akogun, yace Shugaban jami’ar ta Unilorin, VC, Professor Sulyman Age Abdulkareem da tawagarsa sun ziyarce ta sannan ya sha alwashin hukunta dalibin.

Bayan dalibai da malamai sun yi taron dangi sun kamo dalibin
LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: