Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuDalilai Bakwai da ya zama wajibi Uwargida kina buƙatar shan zobo

Dalilai Bakwai da ya zama wajibi Uwargida kina buƙatar shan zobo

Amfanin Zobo ga lafiyar iyali

Zobo da yawan mutane suna shan zobo a matsayin juice mai dadi sai dai wani karin albishir gareku shine baya ga nishadi da zobo ke kawowa yana kuma da matukar amfani ga lafiyar a jikin dan-Adam

Zobo na dauke da sinadarin da dama ga kadan daga cikin su:

vitamin A

- Advertisement -

Vitamin B3

VitaminC

Citric acid

Maleuich acid

Sodium

Kadan kenan daga cikin sinadarin da zobo ke dauke dasu.

Amfanin zobo Kuma a jikin dan Adam sun hada da:

1.Shan ruwan zobo zallah na maganin hawan jini

2. Yana saurin narkar da abinci

3. Ana hada dafaffen zobo tare da habattus sauda da zuma domin magance gembon ciki wato ciwon Ulcer

4. Zobo na dauke da sinadarin da yake rage kiba

5.Yawan shan ruwan zobo na taimakawa wajan kara jini a jiki

6. Har ila yau dai zobo na taimakawa wajan ingantawa da Kuma bada kariya ga ruwan maniyyi

7. Zobo na taimakawa wanda jinin shi yayi kasa sannan kuma yana daidaita jinin.

Uwargida kina da bukatan zobo, citta, kokonba, kanunfari, kankana da sugar domin yin ingantacan zobo juice mai dadi da gina jikin iyalin ki! Da fatan maigida kuma zai taimaka wajen sayo wa uwargida kayan da take bukata domin yin zobo

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: