Dalilan da Jihar Kaduna ta Kara Kudin Makaranta — Kwamishinan Ilimi

A hira da manema labarai suka yi da kwamishinan Ilimi na Jihar Kaduna, Dakta Shehu Usman ya yi karin bayani kan dalilin da ya sa gwamnati ta yi karin kudin makaranta a manyan makarantun jihar, kamar haka:

Dan jarida: Akwai rade-raden Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi karin kudin makaranta a manyan makarantun jihar, shin wasu irin nasarori ko koma baya kuka samu a fannin Ilimi da har kuke ganin ya kamata ku kara kudin makaranta?

Kwamishina: Da zuwan Maigirma Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai abubuwa da dama suka canza a harkar Ilimi, ya zo da sababbin canje canje. Da farko dai a lokacin ne fannin Ilimi ya fara samun kaso mafi tsoka a kasafin kudi fiye ma da yadda aka amince a taronsu na Abuja.

Na biyu, ya sanya fannin Ilimi a shirin ko-ta-kwana, wato ‘emergency’, wanda aka dinga aikin gyaran makarantun, aka dinga yin sababbin gine-gine, aka dinka yin kujerun zama, aka rika girka abinci domin ciyar da dalibai har aka zo matsayin da aka kara kudin da ake siyan littafai. Aka kara kudin da ake kashewa wurin ciyar da dalibai a makarantun kwana. Misalin da nake bayarwa kodayaushe shi ne a yanzu ana kashe kusan miliyan dari takwas wurin ciyar da dalibai. Da a can baya ana karban Naira dubu bakwai da dari biyar amma yanzu ba mu karban ko kwabo kuma yanzu wannan kudin zai zo ya ninka saboda burin da wannan gwamnatin da take da shi na kara yawan makarantun kwana.

- Advertisement -

Sannan ana kashe kudade masu yawan gaske wurin biyan malamai. Mutane na sane kwanan nan muka tallata za mu dauki malaman sakandare 7,600 an yi musu jarrabawa, an gama tantance su domin mu samu mu inganta tsarin karantarwa.

Mun sani cewa a baya an yi ta kuka da wannan gwamnatin cewa ta kori ma’aikata 21,000 amma an manta mun dauki kwararrun malamai 25,000 suka maye gurbin wadancan. Mun kara yawan makarantu a jihar. yanzu haka a shekaran nan ta 2021 za mu bude sababbin makarantu guda shida da ake ginawa, daya a Pambegua, daya a Jere, daya a Rigachikun, daya a Buruku, daya a Manchok.
Sannan muna gina makaranta ta musamman ta zakakuran daliban Jihar Kaduna, wato ‘gifted and talented’ kenan a nan Dan Bushiya. Kuma muna kara yawan makarantunmu zuwa lunguna da sakuna na jihar. Yanzu haka muna da manyan makarantun guda 541 wadanda suke a Jihar Kaduna, ban da makarantun firamare sama da 4,000.

Wadannan nasarorin da Malam Nasir El-Rufai ya samu a wannan dan lokacin ya faru ne saboda irin tunanin da yake da shi na cewa Ilimi ne kadai zai iya inganta rayuwar al’umma ya kai su birnin mun tsira. Shi ya sa kayan karatu da kayan makaranta da kayan karantarwa na kimiyya da fasaha kodayaushe yana cikin kasafin kudinmu kuma shekara ba ta taba wucewa ba mu samu kudin nan mun kashe su wurin wadannan abubuwan ba.

A takaice ina tabbatar muku wannan gwamnatin ta cinma wani zango mai nisa a cikin wannan tafiya musamman da ta mayar da karatun firamare zuwa sakandare kyauta kuma dole a Jihar Kaduna. Yanzu haka a firamarenmu muna da sama da dalibai miliyan daya da dubu dari tara (1,900,000) wadanda suke zuwa makarantun firamare da nazari na gwamnati. Muna dalibai sama da dubu dari shida (600,000) da suke makarantun sakandare. Mun da dalibai sama da dubu ashirin (20,000) da suke jami’ar Jihar Kaduna KASU. Muna da dalibai sama da dubu goma sha hudu (14,000) da suke Kwalejin Ilimi gidan Waya. Akwai dalibai sama da dubu goma sha biyu (12,000) da suke Nuhu Bamalli. Muna dalibai dubu biyar da dari biyar da suke Kwalejin Lafiya na Shehu Idris. Muna da dalibai dubu daya da dari biyar da sittin (1,560) da ke Kwalejin Ungozoma da ke nan Kaduna. Sannan muna da dalibai sama da dubu arba’in da ke makarantun masu zaman kansu.

Ka ga in ka kalli yawan daliban da ke zuwa makaranta a Jihar Kaduna, al’umma ce mai yawan gaske kuma hakkin kula da su yana kan hakkin Gwamnatin Jihar Kaduna. An cinma zango mai nisa kuma gwamnati a shirye take ta ci gaba. Abin da kawai zan kara shi ne duk wanda ya zagaya makarantunmu tun daga Kwalejin Kiwon Lafiya Makarfi zuwa Kwalejin Ungozoma, zuwa KASU inda ake gine gine na mazaunin makarantar na din-din-din zai ga irin yadda ake nutsar da kudi. Haka in ka zagaya sauran makarantunmu. Mutum in yana so ya gani zai iya zuwa makarantunmu ya je GG Kawo, Rimi Kwalej da suk sauran makarantunmu ya ga irin ayyukan da muke yi. Haka kuma in mutum na so zai iya zagayawa makarantunmu na firamare, kwanan nan ma ba a yi ko mako biyu ba muka tura sama da ‘yan kwangiloli dari hudu zuwa ‘site’ domin gina karin azuzuwa a makarantunmu na firamare. Haka kuma nan ba da dadewa ba za mu bayar da wasu ayyukan na kara gina kananan makarantun sakandare guda casa’in. Za mu kara fadada makarantun sakandare kenan da wurin makarantu tamanin. Wannan duk yana cikin burin wannan gwamnati na bunkasa Ilimi a Jihar Kaduna.

Dan jarida: Jama’a na ta korafin ko dan talaka zai iya karatu la’akari da karin kudin makaranta da kuka yi a manyan makarantun

Kwamishina: Maganar gaskiya ita ce Gwamnati ba za ta iya bayar da Ilimi tun daga matakin firamare har zuwa jami’a kyauta ba. Ba zai yiwu ba. Kwanan nan Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya yi magana da al’ummar Jihar Kaduna yana fada musu idan suka je Abuja karbo kason kudin kasa da suke samu daga Gwamnatin Tarayya wani sa’in Biliyan biyar da dubu dari shida (5,600,000,000), wani sa’in da takwas, wani sa’in kasa da haka. Amma abin da gwamnati ke biya a albashi kadai ya zarce sama da biliyan biyar da dubu dari uku. To idan ka yi lissafi za ka ga abin da ya rage maka bai isa ka yi cefane ba musamman cefanen da ake yi a sauran ma’aikatun gwamnati na kayan aiki da sauran bukatunsu na yau da kullum da sauransu balle kuma a ce za a biya ‘yan fansho da garatuti.

Abin da muke so mu yi bayani shi ne a takaice wajibi ne kaima ka bayar da gudummuwarka a matsayinka na dan kasa. Idan danka an ba shi iimi na firamare, da na sakandare kyauta, to in za shi sama haka kai kuma sai ka bayar da naka gudummuwar. Shi ake yi a ko’ina cikin kasar nan, shi ne muka ga mu ma ya kamata mu yi haka. Kuma ko da gwamnati ta ce za ta yi hakan ba za ta iya ba domin ba ta da kudin da za ta iya yin hakan ba.

Dan jarida: Shin wannan dalilin ne ya sa kuka kara kudin makarantar Jami’ar Jihar Kaduna, wato KASU daga Naira dubu ashirin da shida zuwa dubu dari da hamsin?

Kwamishina: Ai daman kudin makarantar Jami’ar Kaduna ba dubu ashirin da shida ba ne. Tun shekara ta 2005, Hukumar gudanarwa ta Jami’ar jihar Kaduna ta tsara za ta karbi kudin makaranta Naira dubu sittin da wani abu. A lokacin nan gwamnatin da take ci a wannan lokacin ta ce mata a’a, ku karbi dubu ashirin da shida da ‘yan kai mu kuma za mu cika muku sauran. Kuma sun cika musu a wannan shekarar, haka kuma da shekara ta dawo sun cika musu. Amma daga nan ba su kara biya ba aka fara mi’ara koma baya suka zo ba su biyan su ko kwabo sai dai su karbi wannan kudin daga hannun dalibai su ci gaba da gudanar da jami’a. Babban abin da suka rika yi a wancan lokacin ba zan ce suka yi ta yaudarar kansu ba, suna yi kamar za su iya suna daddagewa har suka zo yanzu gazawar ta bayyana. Suka tabbatar ba za su iya gudanar da jami’a da wannan kudin ba. Kudin nan in sun karba ba wai kudi ne da za su sa aljihunsu ba, kudi ne da za su biya albashi. To kudin nan in sun tattara shi na shekarar baki daya ba ya isa su biya albashin wata biyu na malaman Jami’ar KASU. To ina za a samo sauran? Saboda haka a koma wancan tsarin. Ina son masu wannan tambayar su sani suna kallon KASU a matsayin wata makaranta ce da ya kamata su yi kyauta. Amma akwai makarantun da na gwammati ne a Jihar Kaduna amma sun fi KASU tsada. Mu je makarantunmu na Ungozoma da na jinya da suke karban Naira dubu tamanin a matsayin kudin makaranta kuma karatun da suke yi bai kai matsayin digiri ba.

Sannan ina so mutane su sani makarantarmu ta kiwon lafiya ta Makarfi babu wani dalibin da ke biyan kudin makaranta kasa da Naira dubu hamsin amma KASU na ana karban dubu ashirin da shida. To so ake yi sai KASU ta durkusa sannan kowa ya dauki dansa ya kai shi Kano, Malaysia ko Sudan? Haka ake so mu ci gaba da gudanar da KASU har sai ta durkusa? Ai wannan ba zai yiwu ba, shi ya sa Allah ya ba wasu jagoranci saboda su yi abin da ya dace.

Bugu da kari ina so mu sani a lokacin da wannan daliban yake KASU yana biyan Naira dubu ashirin da shida, shi kuma a daya bangaren ya karbo sama da dubu dari a matsayin tallafin karatu a wurin gwamnati. Saboda haka ba zai yiwu mu kara kudin tallafin karatu daga dubu goma ko dubu ashirin ba mu mayar da shi Naira dubu dari amma kudin makaranta yana dubu ashirin da shida ba. Muna so mu bayar da Ilimi mai inganci. Muna so KASU ta tsaya da kafafunta ne. Muna so mu bayar da ilimin da  kowa zai rika yabawa har wani ya yi sha’awar kawo dansa. Haka kuma in muka dauki makarantar da ke koyon aikin jinya da ke nan Kaduna, ta Gwamnatin Jihar Kaduna ce suna karban kusan Naira dubu tamanin da wani abu ne. Kwanakin baya suka yi talla za su dauki dalibai masu koyon karatun jinya. Sun sami masu bukatar shiga karatun sama da mutum dubu hamsin. Gurbi kuma guda hamsin suke da shi, idan sun yi kokari shi ne su dauki mutum dari daga baya a rika tafiyar yada kanin wani har a tsaya a hamsin din. To don me za mu rika yaudarar kanmu? Ba gara mu karbi abin da ya kamata su karba ba su kara kayan aikinsu da wuraren karatu, su kara yawan malamai da na’urorin da suke bukata domin hukumar da ke kula da su, su zo su ce yanzu mun kara muku yawa daga hamsin zuwa dari ko mutum dari biyu?
Ita kanta KASUn wadanda suka nemi shiga bangaren likitanci ko hada magunguna suna da gurbin mutum dari biyu misali amma suna da dubban daliban da suka nemi shiga kuma sun cancanta su shiga makarantar amma gurbin da aka ba KASU na daukar dalibai ba zai isa ba. Ka ga da suna da kudi da sun fadada sun dauki sama da dari biyun. Wannan shi ne dalilinmu muna fata jama’a za su fahimce mu.

Da kwalejin Ilimi Gidan Waya, Da makarantar Shehu Idris da ke Makarfi, da Pambegua da nan Kaduna an ba su dama Gwamnati ta fadi mafi karancin abin da ya kamata su caza; jami’a kada ya zama kasa da dubu dari da hamsin. Su za su zauna su duba nawa ne wanda zai dawo yake shekarar karatu na biyu ko na uku zai biya. Nawa ne mazaunin Jihar Kaduna zai biya, nawa ne wanda ba mazaunin Jihar Kaduna ba zai biya? Nawa ne mai kimiyya zai biya, nawa ne mai fasaha zai biya. Nawa ne mai karatun likitanci zai biya, wannan an tura musu. Haka sauran makarantu su ma an yanke musu; masu karatun dufuloma za su biya dubu saba’in kuma daman abin da suke biya kamar hakan ne. Wasu ma fiye da haka suke biya. Sannan babbar dufuloma dubu dari, daman haka suke biya wanda bai sani ba ne yake tunanin an dauki a kara zuwa sama.
Sannan da muka ce su karbi wannan kudin, sai kuma muka hana karban duk wasu kudade domin da in an karbi wadannan kudaden daga baya kuma sai a ce je ka kawo kudin takarda. Je ka kawo kudin fatanya. Je ka kawo kudin sinadari iri kaza da sauransu. Sai muka ce in aka karbi wancan kudin, to kada a kara karban kuma wani kudi. To, wannan ne muke so mutane su gane kuma da yawa sun gane dalilinmu na yin haka. Saboda dalibai sukan fake da wannan suna karban kudi a wurin iyayensu su ce a kawo kudin liman. Su ce a kawo kudin ladan. Su ce a kawo kudin ‘vice chancellor’, rector da provost. Wannan duk karya ce. Wannan dalilin ya sa muka ce duk a hade kudin wuri daya. Ba za a sake rabawa ba balle wani ya samu damar da zai je ya yi karya ya ce an ce ya kawo ‘department’ ko ‘acceptance fee’ duk an soke wannan yanzu.
Kuma ina fatan wadanda suka san kimar Ilimi za su taimake mu wurin bayani saboda da yawa wadanda suka san kimar Ilimi sun dauki ‘ya’yansu sun kai su makarantu masu zaman kansu, sun dauki ‘ya’yansu sun kai makarantu a kasashen waje saboda sun san kimar Ilimi. Amma abin takaici abin haushi irin wadannan su ke zuga talakan da ke kauye kar ya yarda cewa sai ya siyar da gonarsa amma shi ba mu san abin da ya siyar ba ya kai ‘ya’yansa Malaysia ko ya tura su Sudan ko Egypt ko Amurka ko Ingila ba.
A karshe muna fada wa al’ummar Jihar Kaduna cewa, a hukumarta da ke kula da bayar da tallafin karatu ta yi tsari tana bayar da tallafin karatu. Kuma ‘scholarship’ din nan an kara yawan kudin daga dubu goma sha biyar, dubu ashirin zuwa sama da dubu dari. Da abin ba haka yake ba. Sannan in ba ka samu wannan ba, an yi wani tsarin da dalibi zai iya karban bashi wanda ba shi da wani ruwa a cikinsa mutum ya yi karatunsa in ya gama ya biya. Tuntuni ake irin wannan tsarin a kasashen duniya. kuma yanzu an yi tsarin da ba ka bukatar sai ka je wani ofis sannan ka nemi wannan tallafin karatun. Kana zaune a cikin dakinka za ka shiga yanar gizo ka sanya duk bayananka domin neman wannan tallafin. Muna fata al’umma za su yi amfani da wannan dama domin su nemi wannan tallafi su biya wa ‘ya’yansu kudin makaranta. Wanda bai da hali shi ake ba wannan tallafin, wanda kuma yake da hali akwai nasu tsarin na musamman.

Saboda haka ya kamata a yarda gwamnati ta yi iya yin ta, ta dauki tsawon zamani tana yin wannan kuma mun fahimci in ba a yi wannan tsarin ba makarantunmu za su durkushe. Ilimin zai durkushe gaba daya. Kuma ba zai yiwu a yi karya za a yi wani abu ba kuma a kasa yi ba. Abin da ake ce za a yi kuma za mu iya shi ne ilimin firamare zuwa sakandare kyauta kuma za mu iya kokarinmu mu ga iyaye ba su bayar da ko kwabo ba sai dai wanda ya ga dama ta hanyar PTA.

Abu na biyu duk wanda ya san kimar Ilimi ya san bai taba tsada ba musamman in aka kwatanta shi da jahilci.

Na uku, mu sani in muka ce za mu yaudari kanmu mu ci gaba da zama a halin da muke ciki, wadanda suke da hali za su ci gaba da kwashe ‘ya’yansu suna kai wa makarantu masu zaman kansu da kasashen waje, dan talaka kuma ya sha wuya. Shi ya sa muka ga gara kara wannan kudin dan talaka ya samu ingantaccen Ilimi a gida a maimakon komai ya tabarbare ya koma yana neman jami’a mai zaman kanta yana biyan miliyan daya ko miliyan biyu.
Muna tabbatar wa jama’a wadannan kudade da aka kara za a yi amfani da su wurin inganta Ilimi a jami’o’I da makarantunmu, a dauki malamai a biya su hakkokinsu kamar yadda ya kamata. Mun kafa kwamiti su bincika mana hakikanin nawa ya kamata  a kashe wa kowane dalibi, sannan sai mu ga nawa za mu rika bayar da tallafi domin kowane dalibi ya samu ingantaccen Ilimi.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: