Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuDan shugaban Jami'ar Ekiti ya kammala karatu a Oxford

Dan shugaban Jami’ar Ekiti ya kammala karatu a Oxford

Daga Muryoyi

Duniyar sadarwa ta karade da cece-kuce dangane da bullar labari da hotunan dan Shugaban Jami’ar jihar Ekiti wato VC EKSU, Edward Olanipekun, ya kammala karatu a Jami’ar Oxford dake kasar Ingila.

Muryoyi ta ruwaito Jami’ar Oxford na daya daga cikin manyan Jami’o’in da ake ji dasu a duniya.

Olanipekun ya zama shugaban Jami’ar Ekiti tun a 2019 lokacinda tsohon Gwamnan jihar Kayode Fayemi ya nada shi.

Sai dai wannan abu ya daga hankalin wasu yan Nigeria da suke mamakin yadda shugaban Jami’a guda zai dauki dansa ya kai wata kasa karatu a yayinda wasu kuma ke ganin babu wani laifi ko aibu a tare da hakan.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: