Thursday, March 23, 2023
HomeUncategorizedDuba SuDawisu ya lissafa ayyuka Uku da Buhari ke yi wadanda zasu habbaka...

Dawisu ya lissafa ayyuka Uku da Buhari ke yi wadanda zasu habbaka tattalin arzikin Arewa cikin gaggawa

Daga Salihu Tanko Yakasai (Dawisu)
Masoyin Kano da Arewa da Najeriya.

Na yi matukar farinciki da zuwan shugaba Buhari jihar Kano a yau domin kafa harsashin layin dogo wato Jirgin Kasa daga Jihar Kano zuwa Jihar Kaduna, wanda zaa hada shi da na Kaduna zuwa Abuja, daga bisa ni kuma a yi wanda zai tashi daga Abuja zuwa Ibadan, sannan daga can ya hadu da na Ibadan zuwa Lagos.

Amfanin wannan layin dogo ba zai lissaftu ba ko kadan, saboda dumbin alherin da ke cikin sa ga jihar Kano, da Arewa da ma Najeriya baki daya. Banda saukin sufuri da zaa samu na mutane, zaa samu saukin kai kaya da Kano zuwa Lagos ko kuma daga can zuwa Kano. Sannan banda wannan, lodin da ake dorawa titin Kano zuwa Abuja da Lagos shi ma zai ragu sosai wanda zai sa titin yai kargo, sannan kuma wannan layin dogon shine wanda zai hadu da wanda aka kaddamar da aikin sa kwanakin baya daga Kano zuwa Maradi.

A nawa lissafin, aiyuka uku ne na Gwamnatin Buhari wanda zasu kawo habbaka tattalin arzikin arewa cikin gaggawa, aiyukan kuwa sune layin bututun iskar gas daga Ajaekuta zuwa Kano wanda shima Gwamnatin Buhari ke aiwayar da shi kuma aiki yai nisa, sai aikin titin Kano zuwa Abuja wanda shima aikin yayi nisa daga Kano zuwa Kaduna, duk da dai gwamnatin baza ta iya kammala daga Kaduna zuwa Abuja ba kafin karshen waadin mulkin ta, amma dai zaa ci karfin sa. Sai kuma aikin layin dogon da a yau aka kafa harsashin sa. Ribar wannan aiyukan ba na jihar Kano kadai bane, na arewa ne baki daya.

- Advertisement -

Idan Allah Ya bawa gwamnati Buhari ikon kammala wannan aiyukan, sannan kuma Allah Ya basu ikon shawo kan matsalar tsaro, toh cikin kankanin lokaci tattalin arzikin arewa zai mike dodar. Domin bututun iskar gas zai farfado mana da masana’antun mu, wanda su kuma zasu samar da aikin yi da habbaka kasuwanci, titi da layin jirgi kuma zasu habbaka harkar sufuri na mutane da na kaya, dama arewa yanki ne na kasuwanci da noma, wanda duk biyun harkar sufuru shine ruhin su.

Muna kara godewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnatin sa bisa wannan aiki, haka kuma muna kara adduar Allah Ubangiji Ya sa a kammala su gaba daya, arewa da Najeriya mu mora, amin dai!

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: