Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuDCP Abba ya musanta cin hancin da Hushpuppi yace ya bashi a...

DCP Abba ya musanta cin hancin da Hushpuppi yace ya bashi a $1.1million

Daga Muryoyi

Kasurgumin madamfarin nan dan Nigeria da ake tuhuma a Amurka bisa damfarar daruruwan miliyoyi, Ramon Abass wanda aka fi sani da Hushpuppi ya ambaci sunan babban dan sandan Nigeria DCP Abba kyari cikin wadanda ya bawa cin hanci a cikin wata zambar dala $1.1 million da yayiwa wani dan kasuwa a Qatar.

Hushpuppi ya ce ya bawa DCP Abba cin hancin dala $230,000 domin ya kama wani abokin burminsa Kelly Chibuzor Vincent ya garkame a kurkuku. Sauran wadanda ya baiwa cin hancin sun hada da jami’an hukumar St. Kitts and Nevis domin suyi masa takardar zama dan kasa.

- Advertisement -

Sai dai DCP Abba Kyari ya musanta karbar cin hancin ko sisi daga Hushpuppi inda yace Abbas ya same su a ofis a wani lolaci can baya ya shigar da kara kan wani, Kelly Chibuzor Vincent cewa yana yi masa barazana da rayuwarsa.

Muryoyi ta ruwaito Abba ya ce bayan sun kamo wanda ake zargin sai suka fahimci ashe abokinsa ne don haka suka sake shi ya tafi. DCP Abba ya cigaba da cewa kudin da dan damfarar yace ya tura na wasu kaya ne da shi Hushpuppin ya gani a wajen Abba yace yana da sha’awaru kuma Abba ya hadashi da mai sayar da kayan ya saya, ya tura masa kudinsa kai tsaye ta akwunt din shi mai sayarwar.

Hushpuppi dai a yanzu ya amsa laifinsa a gaban wata kotu a jihar California dake Amurka kuma ana sa ran nan ba da dadewa ba kotun za ta sa ranar da za a yanke masa hukunci.

DCP Abba ya nemi jama’a suyi watsi da wannan kazafi da neman bata masa suna “yasan bai karbi ko sisin kwabo a wajen Hushpuppi ba kuma da sauki ma tunda Vincent din da ake magana akai yana nan a raye kuma zai bayar da shaida akan hakan.

Abba ya kara da cewa baya fargaba ko dass duk wanda zai yi bincike akansa ya zo yayi yasan ba za a same shi da laifi ko daya ba.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: