Duka Gwamnoni 36 sun rasa tudun dafawa kan matsalar tsaro -inji Gwamna Darius

Daga Muryoyi

Yan Nigeria sun taso Gwamnoni a gaba bayan da Gwamnan Taraba yayi koke cewa duka Gwamnoni 36 na Nigeria suna cikin wani hali sun rasa yadda zasuyi akan matsalar tsaro da ta addabi jihohin su, domin a cewarsa hannayensu a daure suke basu da yan sandan jihohi, doka ta bawa shugaban kasa komi.

Gwamnan, Darius Ishaku a hirarsa da Channels ranar Alhamis ya kara da cewa yayi ta magiya ga rundunar yan sanda su tsaurara tsaro a bakin iyakokin jiharsa amma babu wani mataki da suka dauka har sai da mayakan “Ambazonian” daga kasar Cameroon suka haura kauyen Manga dake karamar hukumar Takum ranar Laraba suka kashe mutane akalla 11 har da Sarkin garin.

Garin Takum dai shine kauyen da ya sada jihar Taraba da jamhuriyar Cameroun.

Muryoyi ta ruwaito Gwamna Ishaku na cewa a halin da ake ciki duka Gwamnoni 36 na Nigeria sun rasa yadda zasuyi domin shawo kan matsalar tsaro saboda babu yan sandan jihohi.

“Yanzu da ace ina da yan sanda a jiha ta karkashi na ai da umurni kawai zan basu. Je ku tambayi duka Gwamnonin Nigeria wa ke da mafita akan wannan rashin tsaron? Dole sai mun jira abunda Gwamnatin tarayya tayi” a cewarsa.

To sai dai maganar tashi ta jawo jama’a sunyi masu ca, wani mai suna Bafana ya ce “Kaji wani zance, amma a lokacin zabe kun san yadda zaku lallabi jami’an tsaro suyi maku aiki ko?”

Shi kuwa wani cewa yayi ya kamata Gwamnonin su hada kai da Sanatocin jihohinsu domin yin abunda ya dace, ko dai su tsige shugaban kasar ko kuma su kirkiri dokar kafa yan sandan jihohin.

Wasu kuma na cewa kawai Gwamnonin suyi murabus tunda basu da mafita kan matsalar tsaro da aka zabe su domin shi.

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: