Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuEFCC ta kama yan Yahoo 60 a wajen liyafar da suka shirya...

EFCC ta kama yan Yahoo 60 a wajen liyafar da suka shirya zasu karrama wanda yafi iya cuta

EFCC ta kama yan Yahoo 60 a wajen liyafar da suka shirya zasu karrama wanda yafi iya cuta

Daga Muryoyi

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta kama wasu mutum 60 da ake zargi yan fashin intanet ne a wajen wata liyafa da suka shirya domin karrama wadanda suka fi iya zambatar mutane,

Muryoyi ta ruwaito an kama wadanda ake zargin ne a wani Otel dake Abeokuta, jihar Ogun suna tsaka da taron nasu.

- Advertisement -

Taron wanda sukayi basaja suka sanya wa “Peer Youths Awards”, ya samu halartar manyan yan yahoo. EFCC ta ce ta kama su da manyan motoci na alfarma, da wayoyi da sauran na’urori da suke amfani dasu wajen zambatar mutane da yi masu zamba cikin aminci, hukumar ta ce za a gurfanar dasu a kotu da zaran an kammala bincike

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: