Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuMuna fama da rashin tsaro yan sanda na dakon jaka a gidajen...

Muna fama da rashin tsaro yan sanda na dakon jaka a gidajen manya

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce mafi yawan Gwamnoni a fusace suke kuma basu da yadda suka iya ne a bisa abunda ke faruwa na rashin tsaro a jihohinsu domin basu da wani iko kan jami’an tsaro, aikinsu kawai bai wuce su saya masu motoci su zuba masu mai ba amma basu da ikon basu umurni.

Muryoyi ta ruwaito Gwamna El-Rufai a wata tattaunawa da yayi da tashar talbijin ta Chennels yana cewa Nigeria ne kadai a duk duniya da take amfani da tsarin yan sanda na bai daya, (shugaban kasa kadai ke da iko akansu), yace shi yasa kwamitinsu ya dage akan sai an sauya wannan tsari, a bar kowace jiha ta mallaki yan sandan ta sannan kowace karamar hukuma ta samu nata tsarin tsaron.

A cewar Gwamnan zanga-zangar #EndSARS ta fallasa yadda Gwamnoni ke da takaitaccen iko kan sojoji da yan sanda a Nigeria.

- Advertisement -

Ya ce ko kwamishinan yan sanda baka da iko ka bashi umurni, bai zama dole yayi ba kuma ko zai yi sai ya sanar da Sufeta-Janar sai abunda IG ya ce mashi yayi zai yi.

Gwamnan a saboda haka ya ce indai ana so a kawo karshen matsalar tsaro a Nigeria to sai an raba ikon yan sanda a baiwa Gwamnoni iko.

Ya ce mafi yawa an bar Gwamnoni da sayawa yan sanda motoci da sanya masu mai, a yayin da Gwamnatin tarayya ke biyansu albashi.

A cewar Gwamnan yan sanda sunyi karanci a kasar nan saboda haka akwai bukatar a sake dibar yan sanda masu yawa sannan a baza su inda ya dace.

“Yan sanda sunyi karanci a Nigeria, basu kai ko rabin adadin da ake bukata ba sannan kaso mai yawa daga cikin wadanda ake dasu sun jingine aikinsu na yan sanda sun koma daukarwa matan manya jaka” inji Gwamnan

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: