Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuEl-Rufai yace a cire kunya a rika fada masa gaskiya

El-Rufai yace a cire kunya a rika fada masa gaskiya

Daga Muryoyi

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya kalubalanci jama’ar Kaduna su rika fada mashi gaskiya ko bashi shawara ba tare da tsoro ko shakkar komi ba a duk lokacinda bukatan hakan ta taso domin ta haka ne kawai shugaba ke iya gane yana tafiya akan daidai ko akasin hakan.

A wani jawabi da Gwamnan yayi a wajen taron talakawa da masu ruwa da tsaki da shuwagabannin kungiyoyi na jihar Kaduna ya ce “Kar aji kunya, Ni dai nasan ba mai tsoro na tunda tsawo ma bani dashi balle karfi”

Taron dai kusan shine irinsa na 2 da akeyi inda ake hada shuwagabannin kungiyoyin da mata da matasa da jami’an tsaro da sarakunan gargajiya da nakasassu domin bitar kudurorin Gwamnatin da kuma lalubo hanyar kowa zai dandani romon dimokuradiyya a jihar Kaduna

A cewarsa “Ba zan ce wai ana jin tsoron Gwamna ba amma kada a ji kunyar Gwamna ko mataimakiyar Gwamna a gaya mana gaskiya abinda aka gani. Idan matum zai yi zagi ne yayi, zagin Gwamna ba laifi bane kayi ma Gwamna sharri shine laifi amma zagi shugaba dole a zage shi” inji El-Rufai

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: