Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuFasinja ya farfasa kaya a filin jirgin sama na Murtala saboda ya...

Fasinja ya farfasa kaya a filin jirgin sama na Murtala saboda ya rasa jirgi

Daga Muryoyi

Wani fasinja da ba a bayyana sunansa ba ya farfasa tagogi da kayayyakin dubban Naira a filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Mohammed Airport dake Lagos sakamakon rasa jirgi da yayi.

Majiyoyi sun shaidawa Muryoyi.com cewa dakyar jama’a suka ci karfinsa suka kama shi sannan suka mika shi ga jami’an tsaro dake filin jiragin.

Ance mutumin zai bi jirgin Egypt Airline zuwa Cairo amma sai ya makara har jirgin da zai bi ya tashi don haka aka bukaci ya jira jirgi na gaba da zai tashi zuwa kasar Egypt amma sai abun bai yi masa dadi ba inda nan take ya hau dokin zuciya ya shiga barnata komi dake filin jiragen

- Advertisement -

An ga yadda ya rika farfasa gilasan tagogi da na’urori a filin jirgin, Muryoyi.com ta ruwaito sai dakyar aka samu shawo kanshi aka rirrike shi yana haki yana fizge-fizge aka mikawa jami’an tsaro shi.

Jama’a sun tofa albarkacin bakinsu game da aukuwar wannan lamari inda wasu ke zargin ya kamata ayi wa mutumin binciken kwa-kwaf domin da alamu ko wani mugun abun ya boye a jikinsa alal misali ko dan fataucin kwayoyi watakila za a samu matsala idan lokaci ya kure domin yadda yayi abun zargi ne matuka.

 
Wasu kuma na ganin babu wani abun zargi watakila yana sauri ya bar kasar ne domin ya gaji da tsadar rayuwa da juyin-juya hali da bakar wahala da yan kasar ke ciki sai kuma akayi rashin sa’a ya makara sakamkon wani dalili na yanayin kasar

Menene ra’ayoyin ku akai?

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: