Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuFCT ta Gurbace: Mazauna Abuja sun yiwa El-Rufai wasikar dawo-dawo

FCT ta Gurbace: Mazauna Abuja sun yiwa El-Rufai wasikar dawo-dawo

Daga Muryoyi

Ba shakka duk wanda yasan taswira da tsarin babban birnin tarayya Abuja a lokacin da El-Rufai yake minista zai gane irin lalacewa da gurbacewar da tayi a yanzu ta fuskar tsarin gine-gine da kacamewa da cinkoson ababen hawa. Hakan ta saka

Mazauna, Yan siyasa da kuma dattawan Babban birnin tarayyar Nigeria sun fara yin kiraye-kiraye ga tsohon ministan Abuja wanda ke Gwamnan jihar Kaduna a yanzu Malam Nasir El-Rufai yayi wa Allah ya dauki hutu yaje Abuja ya maido masu da ita hayyacinta.

Kiran na kunshe ne a cikin wata zungureriyar takarda wacce tsohon dan majalisa Rt. Hon Dr. Eddie Mbadiwe ya wallafa a manyan jaridun Nigeria,

- Advertisement -

Inda a cikin takardar, Dr. Eddie ya ce suna takaici yadda sannu ahankali kyawun babban birnin tarayyar ya fara dusashewa, yace A lokacinda Malam Nasir El-Rufai yake minista na birnim yayi namijin kokari wajen sauya fasalin birnin tare da bin tsarin da aka kafa Abuja ba tare da sani ko sabo ba,

Dan majalisar ya cigaba da cewa a lokacin El-Rufai ba zaka yi gini akan magudanun ruwa, ko kuwa a wurin da ya kamata ace hanya ce ko wani muhimmim wurin da akayi don saka wani abu ba domin muddin gini ka bai bi ka’ida ba to kan kace kwabo Elrufai zai zo da motocin rusau dinsa (bulldozer) ya jijjige ginin ba ruwansa da ko kai wanene, domin a lokacin har ginin shugaban kasa da ya nada shi, Chief Obasanjo da manyan Janarori na soji irinsu Jerry Useni ya rusa gine-ginensu da sukayi ba a bisa ka’ida ba. Hakan yasa Abuja ta dauki saiti.

Abunda zai baka mamaki da takaici a yan kwanakin nan Abuja ta zama wani kauye marar doka da oda ana rayuwa sakaka, sai rikicin filaye da yayi kamari a birnin, alal misali a filin Gwamnati na Games Village wanda Chief Obasanjo ya samar amma yanzu haka ana ta yayyanka shi ana rikici akai, wasu sun handame shi.

Shaguna ko ta ina birjik ba tsari, garejin gyaran motoci ne, teburan saida kaya ne gasu nan dai birjik a hargitse sun karade ko ina a Abuja ba kyan gani. Ba wai muna yi masu keta bane amma fisabilillahi tsari yana da kyau duk garin da bashi da tsari ko sha’awa baya bayarwa.

Muryoyi ta ruwaito dattijon na cigaba da bayyana takaicinsa cewa da zaka fita karfe 7 na dare a Abuja, to da kuwa da sai kayi kuka da idon ka ko ince da takaici sai ya kashe ka, domin yan Keke Napep da yan Okada wadanda ba ruwansu da bin dokokin hanya duk sararin da suka gani zasu kutsa, zaka ga duk sun haddasa cinkoson ababen hawa.

Kan kace kwabo hawan jinin mutum ya tashi saboda tsananin takaici. Duk da munsan a yanzu aiki yayiwa Malam Nasir El Rufai yawa domin yana fama da wani babban aiki a gabansa na jagorancin babbar jiha mai cike da mabambantan addinai da kabilu wato Kaduna, kodayake dama jarumi ne ya saba, kuma Alhamdulillah yana kokartawa daidai gwargwardo duk da dai ba kowane tsarinsa muke goyon baya ba.

Amma don Allah muna neman alfarma ko zai iya daukar hutu na shekara daya ya zo ya saisaita mana Abuja ya dawo da ita hayyacinta kafin masu fataucin filaye da yan handama su gama gutsuttsura ta suyi watandar ta!

Ina fata sauran jama’a zasu kara da tasu muryar domin sakon mu ya isa inda ake so yaje, a samu a ceto wannan babban birnin mai cike da tarihi da buruka. Ameen daga Rt. Hon Dr. Eddie Mbadiwe, Gogaggen dan siyasa kana shugaban dattawa mazaunin Abuja wanda suka ga jiya suka ga yau suke kuma shirin ganin gobe da yardar Allah.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: