Innalillahi wainna ilaihi rajiun kalli hadarin motar da ya lakume ran mutane 3 a daren jiya a jihar Kaduna
Daga Muryoyi
Akalla kwana 1 kenan da daukar hoton da kuke gani na matasan tare da shugabansu wato Rabiu Biyora. Inda suka sanya a shafin kamfaninsu suna yiwa mutane fatan alkhairi ashe-ashe na bankwana ne.
Muryoyi ta ruwaito hadarin ya rutsa matasan, Usman Bala da Yusuf Yahaya Isa Gama da kuma Babangida Dahiru a bayan ginin majalisa dokoki ta jihar Kaduna
- Advertisement -
Matasan dai sun shiga jihar Kaduna ne domin gudanar da shirye-shirye na taron wata kungiyar marubutan Arewa, mai suna Arewa Writers Association wacce ke da taro a Kaduna ranar Lahadi 13 ga watan Disamba 2020. Kazalika matasan suna aiki ne tare da kamfanin wani matashi a Kano, Rabiu Biyora wato Fafutuka Nigeria Limited.