Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuHisba ta sa wasu matasa karatun Qur’ani a Kano bayan ta kama...

Hisba ta sa wasu matasa karatun Qur’ani a Kano bayan ta kama su suna karta

Daga Muryoyi

Yan Hisba a jihar Kano ta ce jami’an ta sun kama gungun wasu matasa dake tsaka da buga wasan karta inda suka kaisu ofishinsu sannan aka rarraba masu Alqur’ani su karanta.

Hukumar ta zargi matasan da laifin sun bata lokacinsu a banza da wofi wajen buga karta a maimakon suyi amfani da lokacin wajen yin wani abu da zai amfane su.

Muryoyi ta ruwaito sashin Ofishin Hisba na Warawa ne suka kama matasan sannan kodayake an sake su bayan an ja masu kunne sannan an baiwa kowannesu Qur’ani yayi tilawa.

- Advertisement -

Dama ko a watan Augusta da ya wuce hukumar Hisbah a karkashin babban Kwamandanta, Dr Muhammad Haroon Ibn Sina, ta rika kama matasa masu tara gashi ko askin banza a jihar sannan ta haramta amfani da yar tsana wajen saida kaya.

Domin ta ce wannan tamkar yada badala ne.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: