Thursday, February 2, 2023
HomeUncategorizedDuba SuIna da saurayi tsayayye kawai bani da ra'ayin aure ne a yanzu...

Ina da saurayi tsayayye kawai bani da ra’ayin aure ne a yanzu sai nayi Digiri –inji Zee-zee

Daga Muryoyi

Fitacciyar wasan Kannywood Ummi Zee-zee ta musanta labarin da ake yadawa cewa wai tana neman mijin aure, jarumar ta ce sharri aka yi mata hasali ma duk wanda ya santa yasan tana da tsayayyen saurayi wanda yafi son ta fiye da duk wata mace a duniyar nan kuma a shirye yake ya fito kawai dai ita taki bashi izini ya turo saboda sai ta kammala karatun jami’a wato sai ta yi Degree.

Ga abunda Zee-zee ta wallafa a shafinta na Instagram dazu “Salam to Nigerians ni UMMI IBRAHIM ZEEZEE ba Dan jarida ko wani da yayi hira dani nace masa ina neman mijin aure karya akemin domin a followers dina daga cikin masu ilimin wanda suke kula da sa’ido a rayuwata gaba daya sun san cewar ina da saurayina da nake sonsa shima kuma yake sona sosai fiye da ko wace mace a duniya bayan mahaifiyarsa wanda ko gobe nace ya fito muyi aure to zai turo iyayensa gidanmu a mana aure, kawai dai nice bansa aure a gaba na yanzu ba sai na gama karatuna na DIGREE domin ni a makaranta DIPLOMA kawai nake dashi.

Dan haka naji haushi sosai da wannan batun karyar neman mijin da akamin kuma abunda yaban haushi shine da akace ina neman mijin auren da zai ban ci da sha sai kace wata ALMAJIRA ,to ni ci da sha tuni nafi karfinsu wasu ma ciyar dasu nakeyi nagode asha ruwa lafiya”

- Advertisement -

Ummi zee-zee ta kara da cewa “Dan haka duk wanda ya zageni a wannan wata mai daraja ya nunawa mutane shi jahilin addinine kuma uwarsa ya zaga bani ba, kusha ruwa lafiya sai anjima ba jahilin da zan sake replying” inji ta

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: