Irin kokarin da Gwamnatin Jihar Kaduna ke yi don magance mastalar tsaro

Daga Abdullah Yunus Abdullah

Mafi girman ni’ima a duniya sun kunshi abubuwan da suka hada da: abinci da ruwa da sutura da iska da muhalli, kuma duk wadannan ni’imomin ba a jin dadinsu sai da kwanciyar hankali. Ba kuma za a taba samun kwanciyar hankali ba sai da tsaro. Shi kuma harkar tsaro ya rataya ne a kan gwamnati. Hakkin gwamnati ne a kowane mataki na Tarayya, ko na jiha ko kuma na karamar hukuma ta tsare rayuka da dukiyoyin al’ummar da take mulka.

Sai dai babban abin da wasu da dama ba su sani ba shi ne, a tsarin mulkin Nijeriya akwai iya abin da kowane mataki na gwamnati za ta iya wurin kare rayuwaka da dukiyoyin al’ummarta. A tsarin mulkin Nijeriya, duk wasu jami’an tsaro, kama daga soja zuwa ‘yan sanda, har zuwa kan jami’an tsaro na farin kaya suna karkashin Gwamnatin Tarayya ne. Wannan ya hada da daukan su aiki da nada shugabannin wadannan hukumomin jami’an tsaro har da tuttura su jihohi da kananan hukumomin da za su yi aiki yana ikon Gwamnatin Tarayya ne.
Gwamna El-Rufai ko a kwanakin baya ya bulla a kafar talabijin na Channels yana kokawa kan irin yadda gwamnoni ba su da cikakken iko a harkar tsaro a jihohinsu. Ya ce ‘yan sanda da sojoji da duk wasu jami’an tsaro suna karkashin ikon Gwamnatin Tarayya ne sai dai duk abin da wadannan jami’an suke bukata don su gudunar da aikinsu a jihohinsu suna musu.

Gwamnan ya ce dangane da maganar matslar tsaron da ake fama da shi a Arewacin kasar nan kuwa na masu garkuwa da mutane, y ace sun bayar da shawara ya kamata a fito da ‘yan sandan jihohi don su taimaka wa jami’an ‘yan sanda. Sannan kuma in ana so a magance matsalar masu garkuwa da mutane ya ce, ya kamata a yi wani tsari ne na musamman ta yadda za a shiga dazuzzukan Arewacin kasar nan a lokaci daya ana harbin su ta sama, sannan kuma sojojin kasa na bin sauran da suka rage suna kashe su.
Duk masu bibiyan abubuwan da ke faruwa a Jihar Kaduna da kuma kasar baki daya sun san irin yadda matsalar tsaro ya tabarbare a kasar baki daya da kuma irin kokarin da Gwamnatin Jihar Kaduna ke yi don ganin an kawo karshen matsalar tsaro a matakin jiha ta hanyar taimaka wa jami’an tsaro da duk abin da suke bukata duk da cewa gwamnatin ba ta da cikakken iko da sojoji ko ‘yan sanda ko sauran jami’an tsaron da ake turowa jihar yin aiki.
In ba a manta ba, wannan gwamnati ta Malam Nasir El-Rufai da ta zo a shekara ta 2015 ta gaji matsalolin tsaro da dama wanda suka hada da; rikicin makiyaya da manoma da rikicin Kudancin Kaduna da satar shanu da fashi da makami da sara- Suka/ ’Yan-Shara da sauransu. Cikin taimakon Allah wadannan matsalolin duk sun zama tarihi saboda irin kokarin da Gwamnatin Malam Nasir El-Rufai ta yi. Wasu daga cikin matakan da gwamnatin ta dauka har aka samu wadancan nasarori sun hada da:

- Advertisement -

Kafa Kwamitin Tsaro: Abin da Gwamna El-Rufa’i ya fara yi washegarin rantsar da shi, shi ne kiran taro kan tsaro don samo hanyoyin da za a magance matsalolin da suka addabi jihar wanda hakan ya sa ya kafa kwamiti a qarqashin jagorancin Janar Martin Luther Agwai don binciko dalilai da kuma fito da hanyoyin da za a magance wadancan matsalolin musamman rikicin Kudancin Kaduna da yankin Birnin Gwari.

Canja Fasalin Tsarin Tsaro: Gwamnatin Jihar Kaduna ta canja fasalin tsaron jihar inda ta kawo sababbin dabaru ta kuma shigo da Sarkin Birnin Gwari da Sarkin Kagoro cikin Majalisar Tsaro ta Jihar Kaduna don samun wakilcin kowane shiyya na jihar.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta hada kan jihohin Arewa maso Yamma da sauran masu ruwa-da-tsaki don magance matsalar tsaro musamman a yankin Birnin Gwari da iyakokin jihar. Wannan mataki ya taimaka wurin magance satar shanu. Manoma da mutanen yankin sun samu sauqi matuqa duk da matsalar tsaro da yanzu qasar baki daya ke fama da ita.

Zaman Majalisar Tsaro ta Jihar Kaduna duk Talata: Majalisar Tsaro ta Jihar Kaduna wadda ta kunshi shi kansa Mai girma Gwamna da Mataimakiyarsa da shugabannin sojoji da na ’yan sanda da na Hukumar Kiyaye Hadurra da sarakunan Zazzau da Birnin Gwari da Kagoro da duk wadansu masu ruwa-da-tsaki a fannin tsaro na zama duk kusan ranar Talata don tattauna matsalar tsaro da fito da hanyoyin magance su.

Sayo Motoci 192: Gwamnatin Jihar tun daga zuwan ta shekara ta 2015 zuwa yau ta siya motoci qirar Hilux guda 107 da kuma kirar Peugeot guda 85 don a taimaka wa jami’an tsaro don gudanar da aikinsu waxanda yanzu haka ana iya ganinsu rubuce da “Operation Yaqi” suna zirga zirga a lunguna da saqunan jihar. Ana iya cewa baicin wadannan motocin da jami’an tsaro bas u sami motocin fita sintiri ba.

Sayo Babura: Gwamnatin Jihar Kaduna ta samar wa jami’an tsaro Babura domin sintiri.

Sayo Rigunan Sulke: Gwamnatin Jihar Kaduna ta sayo wa jami’an tsaro rigunan sulke don kariya daga harsashi, hakan ya qara qarfafa wa jami’an tsaro gwiwa wurin tunkarar ’yan ta’adda da kare rayukansu.

Kafa Hukumar Sintiri: Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi doka wadda ta ba ta damar kafa Hukumar Sintiri mai suna Kaduna State Vigilante Service. Wannan mataki na kafa Hukumar Sintiri ya taimaka gaya wurin magance matsalar tsaro

musamman ta ’Yan-Shara da qananan varayi da masu shaye- shaye da suka addabi jihar.

Haramta Sara-Suka: Majalisar Zantarwa ta Jihar Kaduna a zaman da ta yi ranar Litinin 27 watan Yuli, 2018 a qarqashin ikon da take da shi na dokar Final Kod “Penal Code” sashe na 60 ta haramta duk wata qungiya ta Sara-Suka ko ’Yan- Shara. Dokar ta tanadi cewa duk wanda aka kama da laifin Sara-Suka zai fuskanci hukunci mafi qaranci shekara bakwai a gidan yari.

Kafa Cibiyar Kyamarorin Daukar Hotunan Sirri (CCTV): Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa wata cibiya ta musamman ta kyamarorin daukar hotunan sirri wanda da ingilishi ake kira CCTV a Abakwa don a rika dauko duk wasu hotuna da bayanan abubuwan da suke faruwa daga lunguna da saqunan jihar. Yanzu haka wannan aiki ya yi nisa sosai, am kafa kyamarorin a cikin garin Kaduna a jiran izini daga hukumar tsaro ta kasa don harba jirage marasa matuka da ake kira ‘drones’.

Kafa Sansanonin Sojoji da ’Yan sandan Kwantar da Tarzoma: Gwamnatin Tarayya da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Kaduna sun samu nasarar kafa sansanonin sojoji da na ’Yan sandan Kwantar da Tarzoma (Mobile Police) a Kudancin Kaduna don magance matsalar tsaro a yankin. Wanda wannan wata babbar nasara ce saboda wani abu ne da ya gagari gwamnatocin baya. Wannan ya daqile faruwar rikicin qabilanci da na makiyaya da manoma da ya addabi yankin.

Sayo Jiragen Sama Marasa Matuqa (Drones): Gwamnatin Jihar Kaduna ta sayo jiragen sama marasa matuqa da suke shawagi a sararin samaniya suna xauko bayanai (drone) don harba su a dazuzzukan jihar domin binciko mavoyar ’yan ta’adda, inda yanzu haka gwamnati na jiran amincewar Hukumar Tsaro ta Qasa ce don fara amfani da su.

Kafa Hukumar Sulhu: Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi doka, wadda ta ba ta damar kafa Hukumar Sulhu (Kaduna Peace Commission) a qarqashin jagorancin shaharraren malamin addinin Kiristan nan Rabaran Josiah Idowu Fearon. Wannan hukuma aikinta shi ne sulhunta duk wasu qabilu ko addinai ko manoma da makiyaya da suke rikici ko suke da wata qullalliya a tsakaninsu a jihar domin a magance faruwar rikici a tsakaninsu a gaba. Sannan su shiga lunguna da saquna su wayar wa mutane kai game da muhimammancin zaman lafiya. A vangare guda kuma suna ba gwamnati shawarwari kan matakan da za ta xauka da za su samar da dauwamammen zaman lafiya a jihar. Shi ma wannan wata babbar nasara ce domin abu ne da aka shawarci gwamnatocin baya amma ba su aiwatar ba.

Kafa Kwamitin Tuntuba da Sulhu ta malamai da fastoci mai suna House of Kaduna Family: Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa wani kwamiti na malamai da fastoci da za su yi aiki karkashin Hukumar Sulhu

Kafa Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida: Gwamnatin Jihar Kaduna ta kirkiro ma’aikata na musamman na harkar tsaro saboda a samu ta rika yin tsare-tsare da tafiyar duk wasu ayyuka na hukumomin tsaro da ke jihar wurin tattaro bayanai na sirri a jihar. Bugu da kari, wannan ma’aikatar ita aka daura wa alhakin kulla kyakkyawan alaka da sauran hukumomin tsaro na Gwamnatin Tarayya da kuma aiki tare da hukumar samar da sulhu ta Kaduna Peace Commission.

Sansanin Sojoji na Forward Operation Base (FOB) a Kafanchan. Gwamnatin Jihar Kaduna tare da hadin gwiwar Gwamnatin Tarayya ta kafa sansanin sojoji a Yankin Kudancin Kaduna. Wannan shi ne sansanin sojoji na farko da aka kafa a yanki na Kudancin Kaduna, wanda sama da shekara 40 ana neman kafawa amma abin ya faskara sai a wannan lokacin. Sannan an kafa wannan irin sansanin na sojojin sama a Birnin Gwari, wanda yanzu haka Gwamnatin Jihar Kaduna ita ta bayar da makaranta a matsayin mazaunin wucin gadi.

Gina Ofisoshin ’Yan Sanda: Gwamnatin Jihar Kaduna ta gina ofisoshin ’yan sanda da dama a faxin jihar musamman inda ake da buqatar hakan. Misali a Karamar Hukumar Birnin Gwari.

Shirin Operation Sharan Daji- Don ganin an magance matsalar tsaro, Gwamna El-Rufai ya yi hadin gwiwa da rundunar sojojin Nijeriya da wasu jihohin Katsina da Kebbi da Naija da Zamfara da kuma Kano don kawo kawo karshen masu garkuwa da mutane da hare-hare na ta’addanci a Dajin Kamuku da kuma Dajin Kuyambana karkashin wani shiri na Operation Sharan Daji.

Shirin Sulhu Da Mika Makamai- Gwamnatin Jihar Kaduna ta fito da shirye shirye da dama na sulhu tsakanin kabilu da su da rashin jituwa tsakaninsu ta hanyar karban makamansu da yin sulhu tsakanin kabilun. Wannan mataki ne da ya taimaka matuka wurin samar da zaman lafiya musamman a Kudancin Kaduna da kuma tsakanin manoma da makiyaya.

Kirkiro Da ‘Yan sandan Jihohi – Gwamnatin Jihar Kaduna ta fara tantance samari a kowane gunduma na karamar hukuma don daukan su aikin ‘yan sand ana jihohi kamar yadda Gwamnatin Tarayya ta fitter da tsarin ta. Wannan shiri ya yi nisa saboda tun kwanakin baya Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta fitar da fom ga duk masu ra’ayi su cike. Yanzu haka an daura wa jami’an tsaro na farin kaya da hakimai da dagatai alhakin tantance wadannan matasan.

Zama da Duk Wasu Zababbu Da Hakimai Na Jihar: A kokarin da Gwamna El-Rufai ke yi na ganin an kawo kaeshen matsalar tsaro a Jihar Kaduna, ya fito da wani tsari na zama da duk wasu zababbu ‘yan majalisa a matakin jiha da na tarayya da kuma hakiman gundumomi don a zauna a tattauna kan yadda za a shawo matsalar tsaro a jihar.

A karshe, duk da wasu matsalolin tsaro da ake fama da su na garkuwa da mutane a jihar da kasar baki daya, ana iya cewa matakan da gudummuwar da Gwamnatin Jihar Kaduna ke ba jami’an tsaro sun taimaka matuka wurin rage rikicin Kudancin Kaduna wurin kwato Shanu a wurin barayin shanu. Jami’an tsaro na Operation Yaki sun samu nasarar kwato shanu da dama a hannun barayin shanun kuma an mika su zuwa ga masu su a wancan lokacin. Irin kokarin da Gwamnatin Jihar Kaduna ke dauka sun taimaka wurin magance sara-suka da ‘yan shara a jiha.

Bugu da kari, wadannan matakan da ake dauka suna taimaka wurin dakile hare-hare na masu garkuwa da mutane da hare-haren ‘yan ta’adda.
Saura da me masu iya magana sun ce, ‘kisan baki sai taro, don haka aikin tabbatar da tsaro ba na gwamnati da shugabanni kadai ba ne, akwai bukatar jama’a su taimaka wajen fallasa miyagun da suke cikinsu ga mahukunta, kuma su guji boye
miyagun saboda dangantaka ko kasancewarsu ’ya’yansu. Ba mu da jihar da ta wuce Kaduna kuma ba mu da kasar da ta wuce Nijeriya. Mu ne kuma kadai za mu hada hannu wajen gyara su.

Abdullah Yunus Abdullah
abdullah.yunus@kdsg.gov.ng

Labarai masu alaka
Comments
Loading...
%d bloggers like this: