Daga Aisha Aliyu Shanono
Kokwamba na daya daga cikin kayan marmari, rabin ta duk ruwa ne Kuma tana dauke da vitamin A,B,C a cikin ta.
Ga kadan daga cikin amfaninta ga lafiyar jiki da kuma abubuwan da za a iya amfani da ita a yau da kullum:-
- Advertisement -
- Warwar gajiyan jiki : Kokwamba na warwar gajiyan jiki dana gabobi, ana so idan mutum yayi aiki ya gaji ya samu kokwamba ya yayyanka yaci tana saukar da gajiya sosai.
- Yawan cin kokwamba na kara lafiyar kwakwalwa.
- Wanke kwanukan da suka yi tsatsa da kokwamba nasa suyi haske kuma su fita tsaf
- Daura kokwamba a fatar idon na tsotse rubabun kitse ya kuma fitar da datti
- Saka kokwamba a kasan harshe akalla na tsawon miti 2 yana dauke warin baki da kuma magance cututtukan dake cikin bakin
- Kokwamba na dauke duk wata kura dake mamaye gilashi ko madubi
- Kokwamba na inganta lafiyar koda wannan ruwan na jikinta yana taimakawa wajan wanke cututtukan dake tare da ita.
Sai mun hadu a maudu’i na gaba tare da ni yar’uwar ku Aisha Aliyu Shanono