Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuIYALI: An Jahilci Aure –Daga Aliyu Samba

IYALI: An Jahilci Aure –Daga Aliyu Samba

Daga Aliyu Samba

Ana gina aure a wannan al’umma don sha’awa, mazan na kallon mata a matsayin wasu abubuwan jin daɗi da biyan buƙata, suma matan na kallon mazan a matsayin haka. An jahilci falsafar aure gaba ɗayan ta, an taƙaita ta akan gundarin sha’awa da biyan buƙata. Hakan ya sabbaba matsalolin da a yau muke kasa maganta a tsarin zamantakewar aure. Rayuwa ce akeyinta ba tare sa soyayya da jinkai ba, kawai dare yayi kazo ka fuskanci matarka da buƙatarka, ko ita ta fuskance ka shikenan an ci moriyar aure.

Shi namiji na kallon kuɗin da ya biya na aurenki a matsayin farashin da aka sanya masa na mallakar mace, ita ma mace na kallon abubuwan da sukai daga bangarenta a matsayin lasisin ya yi mata abinda ta buƙata a matsayinta na matarsa. Zaka tara ma’aurata 1000+, amma basu ma san falsafar aure ba balle aje ga batun ilimin mu’amalar aure, tsarin da addini ya shimfida wajen aiwatar dashi da gudanar dashi ma ba su sani ba, kawai abin buƙata shine wannan jin dadin na ƴan mintuna ƙalilan da samun biyan bukata.

- Advertisement -

Kasuwanninmu cike suke da masu magungunan ƙarfin maza, magungunan dadewa kafin inzali, tsimi na mata, magungunan ƙara girman mama da baya, kwararo kwararo ake bin lungu da saƙo ana saida su ga ma’aurata amma ba a damu da basu ilimin zamantakewa da rayuwar aure ba, ba a damu da nuna musu hikimar da ta sanya akace suyi aure ba, an barsu sakaka kara zube ba tare da wani ilimi da zasu inganta zamantakewarsu takai ba. Wa zamu zarga ko tuhuma a sanda matsalolin mace macen aure suka yawaita? Wa zamu tuhuma idan saɓanin ma’aurata ya kaisu ga kashe junan su, yau miji ya kashe mata, gobe mata ta kashe miji?

Tun ran gini tun ran zane al’umma ta kama wannan hanya, masu ilimin cikinta suka barwa kansu sanin suka sanar da mutane shirme, an rasa inda aka dosa, me aka sa a gaba da ma me akeyi! A haka matsalolin zasu cigaba da ƙaruwa muddin ba a ɗauki gabarar kawo gyara da saita al’amarin ba. Idan munyi da kyau dai zamu ga dakyau.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: