Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuJami'ar Ilorin ta kori dalibin 400L da yayi wa malama duka

Jami’ar Ilorin ta kori dalibin 400L da yayi wa malama duka

Daga Muryoyi

Jami’ar Illorin ta kori dalibin nan na ajin karshe (400Level) mai suna Salaudeen Waliu Aanuoluwa wanda ya lakadawa wata malamar makarantar duka saboda taki amincewa ta taimakeshi kan wani Project da bai samu yayi ba.

Muryoyi ta ruwaito kakakin jami’ar, Mr. Kunle Akogun, ya bayyana haka a wata takardar kora da ya aikewa dalibin.

Ya ce an dauki wannan mataki ne bayan da kwamitin da’ar dalibai na makarantar ya gudanar da bincike kuma aka samu cewa dalibin ya aikata duk abubuwan da ake zarginsa dashi.

- Advertisement -

Sai dai Mista Akogun yace dalibin yana da kwanaki 48 ya daukaka kara zuwa babban kwamitin ladaftarwa na jami’ar idan ya ga ba ayi masa adalci a shara’ar ba.

Idan dai baku manta ba a makon da ya gabata ne Muryoyi ta kawo maku rahoton yadda wani dalibin ajin karshe (400 Level) a jam’iar Ilorin (Unilorin) dake karantar Microbiology, Abdulwaheed Waliu, (Captain Waliu) ya yiwa wata Lakcara mai suna Misis Sakariyah jin-jina saboda taki daga masa kafa kan wani atisaye da bai yi ba.

Jaridar Muryoyi ta bi diddigin rahoton kuma ta ruwaito dalibin ya iske Malamar Misis Sakariyah har Ofishinta ya nemi ta taimaka masa kan wani aikin dalibai na wajibi “Industrial Work Scheme (SIWES) da bai samu yayi ba kuma dama ita ce aka wakilta ta duba aikin nasa wato “Project Supervisor dinsa”

Sai dai ga dukkan alamu Malamar taki bashi hadin kai abunda ya fusata shi tun yana mata ihu yana bubbuga tebur har ta kai ga ya fara sharara mata mari. Bayan yaga ta kidime ta fara kururuwa sai dalibin ya dora da gabza mata naushi, Muryoyi ta ruwaito dakyar lakcarar ta kubuce ta fita a guje zuwa tsakiyar jami’ar tana ihu tana neman taimako amma dalibin ya bita ya cigaba da dukan ta har ta zame ta fadi kasa yana naushin ta, nan da nan tayi jina-jina.

A bidiyon da Muryoyi ta kalla ta ga Malamar warwas a kasa dalibin yana ta dukan ta kafin Dalibai da Malaman Jami’ar suka ankara da abunda ke faruwa suka ruga a guje domin kai mata dauki. Nan da nan sai dalibin ya ruga a guje aka bi shi har aka samu nasarar kama shi. Ita kuma aka kaita wani asibiti dake Jami’ar domin kulawa da lafiyar ta.

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: