Sunday, January 29, 2023
HomeUncategorizedDuba SuJihar Kaduna ta kusa daina dogaro da kason Gwamnatin tarayya

Jihar Kaduna ta kusa daina dogaro da kason Gwamnatin tarayya

Daga Muryoyi

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce nan gaba kadan za ta fara gudanar da kasafin kudin ta daga kudaden da take samu na shiga ba sai ta rika jira kaso daga Gwamnatin tarayya ba.

Bayanin hakan ya fito ne daga Kwamishinan kasafi da tsare-tsare na jihar, Muhammad Sani Dattijo a wajen taron jin ra’ayoyin jama’a game da kasafin 2022 da ya gudana ranar Talata a majalisar dokokin jihar Kaduna.

A cewar Dattijo Gwamnatin jihar Kaduna tayi nisa wajen ganin ta cimma wannan kuduri nata na dogaro da kai kuma hakan ya faru ne a sakamakon irin goyon bayan da majalisar dokokin jihar ke baiwa fannin zartarwar jihar.

- Advertisement -

Kwamishinan ya ce a hawan Gwamnatin APC a karkashin Nasir El-Rufai a 2015, kudin shigar da suka iya tarawa bai shige N13bn ba a duk shekara amma a yanzu jihar Kaduna na samun kudin shiga da ya kai N57bn

A cewar Dattijo nan gaba kadan duk kudin da ta samu daga Gwamnatin tarayya zai zama rara ne ko kari kawai

LABARAI MASU ALAKA

Leave a Reply

- Advertisment -

MAFI SHAHARA

RA'AYOYIN JAMA'A

%d bloggers like this: